Tuesday 22 June 2021

YADDA AKE KUNUN AYA


Aya ta kasance abu mai amfani ga lafiyar dan adam ta kasance tanada dandano mai gardi aya tana dauke da sinadadin magnesium,calcium da kuma iron tana samar wa jiki sinadarin protein tana kunshe da sinadarin vitamin B wanda yake amfanar da fata da gashi,haka zalika aya tana tsawaita kuruciyan mutum haka zalika aya yanada amfani sosai ga mata mussaman masu aure domin ya kasance abu mafi inganci da yakamata su rika sha a koda yaushe.haka zalika kanumfari da citta su nada matukar amfani ga lafiyar mu wajen karemu daga shigan sanyi jikinmu. shiyasa  tattaunawa namu na yau na kawo muku yadda ake kunun aya.

ABUBUWAN BUKATA SUNE 

Mudu daya na aya 

Ruwa 

Madara 

Dabino 

Suga 

Kwakwa 

Kanumfari 

Citta danye ko bushashshe

YADDA AKE HADAWA 

Zaki dau bushashshen ayanki ki surfa sai ki jika shi da ruwa mai dan yawa,sai ki bari ya jika sosai sai ki tsantsameshi gaba daya sai ki ajiye a gefe,sai ki dau kofi 4 na ruwa ki zuba a ciki bayan haka zaki samu kwakwa naki shima ki wanke sai ki zuba cikin ayan,sai ki wanke dabino naki tare da cire kwallayen cikinta sai ki jikasa shima domin shima yanada tauri sosai,sai ki dauko ginger da kanumfari naki duka sai ki zuba a cikin jikakken ayanki bayan kin gama hada komi sai ki saka a blender naki ki tabbata kin wanke shi kuma baa markada kayan miya a ciki zaki markadeshi har sai yayi laushi sosai sai ki ajiye a gefe, sai ki dauko baho naki da abun tacewa sai ki fara diba kina tacewa har sai kin gama tacewa gaba daya sannan ki zubar da diddigin ayan a shara. Idan kika gama kikaga bakya ganin diddigin aya toh ya tacu sai ki dauko suga naki ki zuba dai dai yadda kikeso,wasu basa ma saka suga saboda zakin dabino dake cikinta ma ya wadatar haka zalika zaki iya saka flavour a ciki idan kinaso don ya kara masa kamshi sai ki zuba a gora ko a jug ki saka a fridge,domin shi kunun aya yanason waje mai sanyi ne in ba haka ba zai iya lalacewa minti kadan idan zafi ya masa yawa.


BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR 


No comments:

Post a Comment