Kunun Aya na daya daga cikin abun sha
mai farin jini sosai ba a nan kadai arewacin nigeria ba, a qasar gaba daya. Ana
yin kunun aya ne daga Aya (tiger nuts). Yana da dadin sha da sanyaya jiki da
makogwaro.
Abubuwan da ake bukata domin hada
kunun aya sune kamar haka.
- Aya
- Madara
- Kwakwa
- Dabino ( busashe)
- Citta
- Sugar
-Rake (sugar cane)
- Flavour
Yadda ake hadawa;
Da farko za mu debo Aya daidai yadda
ake bukata a jika ta. In ayar ta jiku sai a wanke a rairaya a cire kasa da
kananan duwatsu. Sai a bare dabino mai dan yawa a cire kwallon a zuba a kan Aya
din. Sai a babbala rake da wuka a zuba,Sai a saka citta akai nika.
A bare kwakwa a gurza a grater sai a saka a blender a nika sosai, in an kawo kullun ayar da aka nika sai a hada da wannan kwakwar a kara ruwa a tace su, sai a saka flavour da aka fi so, (Banana flavour yafi dadi) da sugar. Wasu sukan matse ruwan rake su zuba basu sakawa a nika su tare kamar yadda nafada daga farko.
Mu sani cewa kunun Aya na son sanyi
sosai,,saboda haka kullum ya kasance cikin sanyi domin yana saurin lalacewa
kuma bata da dadin sha in babu sanyi sosai.
Daga Maryam Idris.
No comments:
Post a Comment