Tuesday 23 February 2021

Yadda Ake Hadda Milkshake in Strawberry Da Dabino















iyayan itacen strawberry da kuma dabino suna da matukar amfani da muhimmanci ga lafiyar jikin mutum.

Shi Dabino na da tsohon tarihin da wasu 'ya'yan bishiyan ba su da shi, ba wai yanzu ba ko tun da can mutane sukan dauke shi a matsayin abinci, za kuma a iya cewa yana gaban duk wani dan itace, masamman sabo da sukarin da ya tattara a cikinsa, wannan zakin ya shafi busasshe da danye wanda ya nuna. Haka ma hukumar kula lafiya ta Amurka ta bayar da shawara ga matasa da cewa, wanda ya ke cin dabino zai sami duk abin da ya ke bukata na Magnesium, Manganese, Copper, zai sami kusan abin da yake bukata na rabin sinadaran Potassium da calcium.



















Iyyen itacen strawberry kuma yana tattare da sinadarai dake taimakawa zuciya da tsarin jinni a jiki, yana karfafa hakora da kasusuwa, yana gyara fata da rage tsufa a fata, yana kuma tattare da bitamin c mai yawa wadda ke karfafa garkuwan jiki.

 



















Abubuwan  bukata sune:

·      Dabino

·      Strawberry

·      Madara

·      Kankara

 


















 yadda ake hadda milkshake in strawberry da dabino

1.    Da farko zamu jika dabinon mu idan har abun nikanmu[blender] ba mai karfi bane amma idan yana da karfi ba sai mun jika ba.















2.    Zamu zuba jikakken dabinon mu da strawberry da kankara da madara acikin blender, zamu iya amfani da madaran ruwa ko mu samu madaran gari mu kada da ruwa mu zuba sai mu nikasu tare.















3.    Mun kamala milkshake in mu na strawberry da dabino. Sai mu zuba akofi musha shi da sanyin shi.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho

YADDA AKE HADDA MIYAN WAKE A SAWAKE



 

Shi de wannan miyan, anna bukatan wake wadda shine mafi muhimmaci wajan hada miyan  yayyin da sauran abubuwa da za,a sa aciki zasu kara masa dandano da kamshi ne.

Wake na tattare da sinadarai irinsu protein, dietary fiber,  B vitamins da wasu  sinadarai masu  muhimmanci da tarin yawa, wadda ke taimakawa wajen wanke ciki (bahaya) musamman ga yara kanana, Yana rage taruwan kitse a jiki, yanna Samar da kariya akan cutar siga kuma yana samar da sauki wa mutanen dake fama da cutar siga sannan yanna Kawar da cutar daji.
Ga mata masu juna biyu cin wake yana karawa mata jini , lafiya , yana karawa yaron da yake cikiin ta lafiya da kaifin basira .

 

ABUBUWAN BUKATA SUNE:
Wake
Tattasai
Attarugu
Albasa
Kanwa
Manja
Sinadarin dandano
Crayfish
Bushashen kifi
Ruwan 

 

YADDA AKE HADDA MIYAN WAKEN
1. Da farko zaki markade tattasai, attarugu, da albasan ki.
2. Sai  ki wanke waken ki ki cire bawon wanken tas saiki zuba waken ki a tukunyan miyanki kisa kanwa dan kadan  da ruwa ki dafa.

 

3. In ya dafu saiki zuba markadadden kayan miyan ki a ciki da manja da sinadarin dandano da crayfish sai kiyi anfani da muburgi ki burge waken ki.
4. Saiki dauko bushashen kifin ki kisa a ciki saiki bar miyanki ya dan kara dafuwa.


 

5. Shikenan miyan waken ki ya haddu zaki iyya cin miyan da tuwon shinkafa, tuwon masara ko tuwon eba.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

YADDA AKE HADDA GURASA BANDASHE

Gurasa sananen abinci ne a arewacin nijeriya wadda ake amfani da flawa wajan hadda ta kuma ake kwadata da kuli-kuli ko a ci shi da tsire ko balangu.















ABUBUWAN BUKATA SUNE:

·         Flawa

·         Yeast

·         Ruwan dumi

·         Man gyada

·         Gishiri

·         Sikari

·         Kuli kuli

·         Garin yaji

·         Sinadaran dandano

·         Albasa

·         Kabeji

·         Tsire ko balangu

·         Tumatir











YADDA AKE HADDA BIREDIN GURASAN

1.      Da farko zaki hadda flawa,gishiri,yeast,sikari guri daya ki gauraya saiki zuba ruwa lab lab sai ki kwaba flawan ya haddu.

2.      sannan ki zuba dan man gyada, ki kuma kwaba shi na minti biyar sai ki bar kwabin ya huta kuma ya tashi na sa’a daya.

3.      Bayan awa daya ki daura tukunyan gashin ki a wuta yayyi zafi, sai ki dibi kwabin flawan ki a tafin hanun ki ki fadada shi yayyi zagayye watto round saiki daura akan tukunyan gashin ki, ki rage wutan sai ki barshi ya gasu.














4.      Bayan yan mintina sai a juya flawan zuwa dayan bangaren  a gasashi, sai a sauke haka za ayi tayi har zai kwabin flawan ya kare.

5.      Toh biredin gurasan mu yayyi.










YADDA AKE HADDA BANDASHEN GURASA

1.       Zamu nika kuli kuli da sinadaran dandano da garin yaji.

2.       Sai mu yanka albasa, kabeji, tumatir da tsiren mu.

3.       Sai mu dauko gurasan mu, mu dangwala a ruwan zafi sai mu cire mu kuma dangwala shi a cikin hadin kuli kulin mu. Haka zamuyi ma duka gurasan mu har sai ya kare kuma sai yaji kuli kuli sosai.














4.       Sai mu zuba man gyadan mu da muka soya da kabeji,tumatir,albasa da tsire akan gurasan da yaji kuli kuli mu gauraya ko ina yajji.

5.       Toh bandashen gurasan mu ya kamalu sai ci.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho