Tuesday, 27 July 2021

TSOHUWAR JARUMAN FINA FINAN HAUSA MANSURAH ISAH TAYI ZAZZAFAN MARTANI KAN RABUWAN AURENTA.

Fitacciyar jaruman finafinan hausa kuma tshohuwar matan jarumi sani danja mansurah isah tayi Allah wadai da irin kalaman da mutane keyi mata na suka domin ta fita daga gidan mijinta. A karon farko kenan da jarumar ta fito ta kuma maida wa wadanda ke sukarta martini inda take cewa maganganun da sukeyi na sukarta ya isa haka domin kuwa ba akanta aka fara saki ba.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta cewa; tayi hoton sallah ance abinda yasa ta fito kenan,tayi tafiya zuwa wani gari ance shiyasa ta kashe aurenta,taje cin abinci da kawayenta ance iskancin da take sonyi kenan,taje aikin NGO na rabo da ta sabayi sama da shekara 20 kenan tana wannan rabo ance daman yawon daya fito da ita kenan. Sa’annan jaruman tace saki ba haramun bane don manzon ALLAH ma yayi kuma shi muke koyi dashi. Mansura ta kuma cewa ba ita kadaice mai aure da aka fara saka ba, tace idan mutane sunga yayan masu kudi tsirara ko ba dankwali a kansu ba’a Magana sai dai a yabesu,amma in har yar film tayi wani abu sai a zageta,wannan ba adalci bane.

Tsohuwar jarumar ta kuma shawarci mutane da suji tsoron Allah domin daga yara har tsofaffi suna bibiyanta suna zaginta,tace su tambayi na kusa dasu yadda zafin saki yake suji domin sanin illar abinda suka mata. A karshe jaruman tace Allah zai saka mata,kuma bazata taba yafewa duk waenda suka shiga rayuwarta ba, Alla kuma ya jarabcesu da kuncin rayuwa na aure domin su gane kuskurensu.AMEEN YA ALLAH.

BY: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR

 


Wednesday, 14 July 2021

Yadda ake hadda miyan karas

 


Miyan karas, miya ne dake cike da dandano, kuma miya ne da idan kika gwada zaki so ki kara.

Binciken kimiyya ya bayyana cewa bayan karin dandano da karas yake karawa abinci yana kuma dauke da sinadarai masu yawa da suka hada da antioxidants, beta-carotene, alpha-carotene, lutein, potassium, vitamin C, vitamin A, fibre da Carotenoids.Abubuwan bukata sune:

·         Karas

·         Albasa

·         Curry

·         Gishiri

·         Tafarnuwa

·         Attarugu

·         Sinadarin dandano

 


Yadda ake hadda miyar karas

1.    Ki samu tukunyan ki mai tsafta, ki sa a kan wuta.

2.    Sai kisa man zaitun idan baki dashi zaki iya sa man gyadan ki.                                                   


3.    Ki zuba albasan ki a cikin man ki soyashi sama sama yayyi laushi amma kar ya kone.

4.     Idan albasanki yayyi laushi sai ki zuba sinadarin dandanon ki,gishiri,tafarnuwa da curry mu soya na minti daya.                                       


5.    Sai mu zuba karas in mu da muka yayyanka a ciki da ruwa mu barshi ya dahu.

6.    Idan ya tafasa kuma karas in mu yayyi laushi sai muyi amfani da hand blender mu markade shi a cikin tukunyan ko kuma mu juye komai a blender mu nika.    


7.     Bayan mun nika sai mu mayar dashi  kan wuta mu zuba dan attaruhu idan miyan mu bai ji gishiri ba sai mu kara mu barshi na minti daya.

8.    Toh miyan karas in mu ya hadu, ana shan miyan zalla ne, ga daddi  ga amfani ga lafiyar jikin mu.

   

Marubuciyya: Firdausi Musa Dantsoho

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tuesday, 13 July 2021

Ya Kamata shugaba Buhari Ya Rika Yi wa yan Kannywood Ta’aziyyar rasuwa inji Mansurah Isah

 Tsohuwar Jarumar masana’antarshirya fina-finan hausa ta kannywood, Mansura Isa ta yi ƙorafin tare da nuna rashin jin dadin ta  bayan da  shugaba Buhari ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga mawaki Abdulganiyyu da aka fi sani da Sound Sultan ta hannun Femi Adesina.
Tsohuwar jaruman ta bayyana hakam a shafin nata na Instagram inda ta wallafa rubutu kamar haka; Baba Buhari, tin da a ke mana Mutuwa a Kannywood ba ku taɓa mana jaje ba, ko gaisuwa na rashi ba. Amma duk sanda yan Kudu wani abu ya samesu ku ne na farkon jaje.In baku jawo naku a jiki ba, wa za ku ja jiki ? Masu girma Dr Zainab Shinkafi da Mamanmu Aisha Buhari ne kadai su ke bamu goyon baya kuma muna yaba musu.
Amma za mu ji dadi in ka nuna mana ƙauna muma Baba Buhari.”
Mansura ta cigaba da cewa; Mu ne ku fa, duk Alheri da muka samu AREWA muke kawowa domin a amfana. Dan Allah a duba wannan Abu Baba.Daga ƙarshe dai Mansurar ta ce ta karkata akalar sakon zuwa Bashir Ahmad, daya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Buhari a fannin yada labarai.
“Bashir Ahmad, kai ne ya kamata ka yi wannan, domin shima Adesina yana gyara nasu mutanen. Kuma ina da yakini cewa kasan irin gwagwarmaya da muke wa gwamnatin nan, duk da zagin mu da a ke yi a kanku. Dan haka muna jiran sakon ta’aziyyarmu ga wadanda muka rasa musamman ta mamanmu Haj Zainab Booth.

Marubuciya: Firdausi Musa Dantsoho

Monday, 12 July 2021

Allah Yayiwa Babban Mawaki Sound Sultan Rasuwa.


Yan Nigeria na cike da alhinin rasuwar babban mawakin turanci da yaren yarbawa, Olanrewaju Ganiu Fasasi wanda aka fi sani da sound sultan.

Mawakin ya rasu ne a ranar lahadi 11, ga watan yulin 2021 sanadiyar cutar kansa mai suna angioimmunoblastic t-cell lymphoma kamar yadda yayansa Dr. Kayode Fasasi ya wallafa a wata sanarwa daya fitar a ranar lahadin sanadiyar rasuwar qaninsa din.

Mawakin ya rasu yana da shekaru 44 kuma yabar mata daya da yara uku da yan uwansa maza da mata. Muna fatan Allah yayi masa rahmah

 Daga Mayam Idris

Friday, 9 July 2021

Yadda ake hada lemun pina colada

 


Ayau, zamu kawo maku yadda ake hadda lemu mai daddi da saukin haddawa.shi wannan lemun babu giya a ciki ko kadan kuma zamuyi amfanin da iyayan itace wadda suke da amfanin ga jikin dan adam.Abubuwan bukata sune:

·         Abarba

·         Madaran kwakwa watto coconut milk

·         Lemun abarba

·         Siga

·         kankara


yadda ake hada pina colada

1.       zaki zamu blender inki mai karfi wadda zai  iyya jure wahala sai ki zuba abarban ki mai kankara.

2.       Bayan kin zuba abarbanki sai ki sa kankara, madaran kwakwanki,lemun abarba da siga ki nika su gabaki daya.


3.       Toh lemunki ya hadu sai ki samu kofin ki, ki zubz a ciki kasha da sanyin sa.

 

Marubuciyya: Firdausi Musa Dantsoho

YADDA AKE HADA GAS MEAT


 

Abubuwan bukata sune:

·         Nama

·         Albasa

·         Bakin masoro

·         Gishiri

·         Kanunfari

·         Kuli2,

·         Ruwa kadan.

·         Tafarnuwa

·         Garin kuli-kuli

·         Man gyada

·         Garin yaji


Yadda ake hada gas meat

1.    Zaki yanka naman ki sala-sala sai ki samu sinadarin dandano, masoro,gishiri, garin yaji da tafarnuwa , ki zuba a cikin naman ki jujuya sai ki rufe ki barshi na minti talatin.

2.    Sai ki nemi tukunya ki zuba namanki da kikayi mai hadi a ciki, ki rufe har sai ruwan naman ya fara fitowa.

3.    Sai mu zuba yankake albasa,man gyada da garin yaji mu  juya.

4.    Sai  ki zuba ruwa kadan ki rufe ya dahu na minti goma.

5.    Bayan minti goma sai mu zuba garin kuli-kuli muyi ta juyawa har sai ruwan naman ya tsose amma ba duka ba toh gas meat inki ya haddu.

6.    Kiyi serving da tumatur da albasa da dafaffen dankali.   

 

Marubuciyya: Firdausi Musa Dantsoho

Yan fim mutani ne kamar kowa zasu iya yin kuskure a daina yin masu kallon yan iska. inji Hauwa Waraka

 


Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai hausa  ta Kannywood, Hauwa Abubakar, wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta yi kira ga masu cewa yan fim musamman mata yan iska ne, da su daina yi musu irin wannan kallon, domin kuwa su ma mutane ne, kamar kowa za su iya yin kuskure kuma za su iya yin dai dai, don haka sai a rinka kallon su kamar sauran mutane in dai adalci a ke so a yi musu.jaridar dimokuradiyya na ruwaito.


Hauwa Waraka jarumace da  ta ke taka rawa a cikin yawancin fina-finan hausa da ta ke fitowa, musamman ma wadanda ta yi suna kuma ta fito a karuwanci da shu’ummanci, a hirar da akayi da ita wadda aka tambayeta game da rol in da take yawan fitowa ta bayyana cewa , “Ba hali na ba ne, yanayin rol din ne haka, kuma idan za a kalle ni a matsayin karuwa ai na fito a fina-finan da dama a wata siffar. Ka ga na fito a matar aure mai hakuri da biyayya ga mijin ta da iyayen ta, don haka fim ne ya ke zuwa da haka” inji ta.


Ta ciga ba da cewa, ” Amma yanzu da mu ke magana da kai a natse ka same ni, don haka rayuwar cikin fim daban, wadda mu ke yi a waje daban, domin a fim ana son a nuna fadakar wa ne, yadda mutane za su fahimci sakon, don haka masu kallon mu su gane abin da mu ke yi a fim rayuwar mu ba haka take ba”
A karshe ta ce, “Don haka a daina yi mana kallon ‘yan iska, don babu wanda ya ke so ya ga ya lalace ko wani na sa, don haka idan aka ga mun yi ba dai-dai ba, to a rinka yi mana addu’a ta alheri, ta haka ne za mu gyaru.


Marubuciyya: Firdausi Musa Dantsoho

Monday, 5 July 2021

Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Booth rasuwa

 


Allah Ya yi wa fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hajiya Zainab Musa Booth rasuwa. Zainab Booth ta rasu ne a daren ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli a jihar Kano.

Marigayiyar ita ce mahaifiyar shahararrun ’yan wasan Hausa uku wato Maryam Booth, Ramadan Booth da kuma Amude Booth.

Jaruma Maryam Booth ce ta sanar da rasuwar mahaifiyar tata a shafinta  na Instagaram.Mabiya shafinta na  Instagram da abokanayan sana’anta na Kannywood da nollywood sun yi tururuwa wajen aika sakon ta'aziyya da jaje ga jaruman da iyalanta.

A ranar Juma'a 2 ga watan Yuli ne aka yi jana'izar tauraruwan wasan kwaikwayo na hausa, Zainab Booth, wacce ta rasu a ranar Alhamis, a birnin Kano aka birne marigayiyar wacce ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.Daruruwan abokan aikinta da masu aiki a masana'antar fim, irin su Ali Nuhu, Falulu Dorayi da Yakubu Mohammed da masoya da dama sun hallarci jana'izar. Marigayiyar ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Domin tunawa da marigayiyar jarumar, jaruman Kannywood maza da mata da dama sun wallafa hotunanta a shafukansu na sada zumunta. Dan uwanta, Ramadan Booth, shima ya yi addu'ar Allah ya jikarta da rahama ya gafarta mata. Marigayiya Booth ta rasu ta bar yara hudu; biyu maza da biyu mata.

Marubuciya:Firdausi Musa Dantsoho

Jarumin Bollywood Aamir Khan da matarsa Rao sun rabu bayan shekaru 15 da aure

 


Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Amir Khan ya sanar a ranar asabar uku ga watan yuni da cewa zai rabu da matar sa da suka yi shekara 15 da aure watto mai shirya fim Kiran Rao, kamar yadda `The Guardian ta ruwaito.  ma'auratan sun sanar da rabuwar su amma sun yarda zasu ci gaba da kula da dan su kuma zasu ci gaba da wasu ayyukan tare.Sun bayyana  cewa : "A tsawon shekaru goma sha biyar [15] da muka shafe tare mun karu da juna sosai yayyin tafiyar da rayuwan mu cikin walwala da raha, kuma alakar mu ta ginu cikin aminci, girmamawa da kaunar juna." "Yanzu muna bukatar bude sabon shafi a rayuwar mu -- amma ba a matsayin mata da miji ba, sai dai matsayin iyaye da kuma iyali ga kowannen mu." Khan da Rao sun hadu ne lokacin daukar wani fim a shekarar 2001 kuma Rao ce mai taimakawa mai bada umarni, kuma suka yi aure a watan Disambar 2005. Jarumin mai shekaru 56, wanda fim dinsa na dambe, 'Dangal' ya maida shi babban tauraro a kasar China, sun rabu da matarsa jaruma Reena Dutta a 2002.Ma’auratan sun ce"Mun fara shirye shiryen rabuwa wasu lokuta, amma yanzu ne muka ga dacewan mu zartar da wannan hukunci, na rayuwa ba a tare da juna ba, amma zamu cigaba da gudanar da rayuwa yadda ta kamata tare," Khan da Rao suka ce."Zamu kasance iyayen masu kula da dan mu Azad, wanda zamu raina kuma ya tashi a hannun mu. Za kuma mu ci gaba da aikin hadin gwiwa a fim, gidauniyar Paani da sauran ayyukan da muke da sha'awa." Khan da Rao yar shekara 47, sun godewa yan uwa da abokan arziki "wanda a cewan su da babu su baza su iya yanke hukunci cikin salama ba." "Muna rokon masu fatan alheri da su yi mana fata na gari, kuma tare da fatan za su gane ba mun rabu ne har abada ba, hanya ce ta fara sabuwar rayuwa."

Marubuciya: Firdausi Musa Dantsoho

 

Har yanzu ana ya yi na a masana’antar Kannywood inji jaruma Fati Bararoji

 Tsohuwar jaruma fina-finai hausa ta Kannywood wadda har yanzu ake damawa da ita a masana’artan watto Fati Baffa Fagge, wacce a ke wa lakabi da Fati Bararoji, Ta bayyana cewar ita fa har yanzu ba ta yi tsufan da za a daina yayin ta ba a cikin masana’antar, domin kuwa, har yanzu a na damawa da ita kamar lokacin kuruciyar ta.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar da tayi da jaridar Dimokuradiyya, dangane da har yanzu irin su da suka dade a harkar ba su bar wa yan baya ba, watto jarumai da suka shigo harkar a yanzu, kasancewar su jaruman da suka ci lokacin su a baya.


Sai dai Jarumar ta yi saurin bada amsa da cewar “Sam babu wani lokacin mu da za a ce mun ci a baya, kuma yanzu mun zo muna cin na wasu, domin babu wanda ya ke cin lokacin wani, don haka yanzu ma lokacin mu ne.” Inji ta.
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ba a fiye ganin ta ba sosai, sai ta ce “Ai da ba a gani na, ba Wai na daina fim ba ne, wasu harkokin kasuwancin da na ke yi ne, su ka sa ba a gani, don kada na karbi aikin mutane ya zama ban samu zuwa ba, Amma da ya ke a yanzu ina samun lokaci ai ga shi ana gani na, don haka babu wani-daina yayin mu da aka yi, kuma har yanzu muna cin lokacin mu ne.” Kamar yadda ta ce.Daga karshe ta yi kira da masoyan ta da su ci gaba da kallon fina-finan da za su fito nan gaba, domin za su ci gaba da ganin ta musamman fina-finan da a ke haskawa a gidajen talbijin manya, irin su Arewa 24 da sauran su.


Marubuciya: Firdausi Musa Dantsoho