Aure wata alaka ce tsakanin mace da namiji wadda yake nufin hada rayuwarsu ta zama daya,hakanan kuma makomarsu ta kasance daya. Ana yin aure domin abubuwa da dama ,daga cikinsu akwai kariya daga zina,samun nutsuwa da kwanciyar hankali,samawa abunda aka Haifa mutunci da sauransu. Aure a musulunci wani hanya ne wadda yake halattawa namiji da mace neman junansu haka kuma sunnan annabi ne wadda yake wajibi ga duk mai iko yayi shi, kowace irin al’umma akwai matsayin da ta bawa aure haka nan kuma kowace al’umma akwai yadda take tafiyar da nata yanayin aure.
Haka zalika duk wani namiji ko mace da ta kai wani munzali na manyance abu na farko da ake mata fata shine samun miji na gari. Haka kuma bisa al’adar kasar hausa namiji ne yake ganin mace idan hankalinsa ya kwanta da ita sai ya tura iyayensa a nema masa izini har akai matakin soma batun aure.wasu lokutan kuma iyaye ne ke zabawa yar su mijin da sukaga ya dace ta aura, Haka zalika akwai wasu muhimman matakai da ake bi wajen neman aure musamman a kasar hausa wadda kafun miji ya auri mace ko mace ta auri namiji sai an duba su, musamman ga y’a mace wadda iyayenta bazasu so ta auri namiji mayaudari ko bata gari ba, haka kuma suma wajen miji bazasu so dansu ya auro mace mara tarbiyya ba.
1) Mataki na farko shine bincike kan asali wadda a al’adan bahaushe aduk lokacin da namiji ya fara nema aka masa iso toh iyayen yarinya sukan fara bincike akansa saboda sanin asalinsa da kuma inda ya fito domin a tabbatar da zancen da yake gayawa yarinya gaskiyane ko karya.
2) Na biyu shine halayya da dabi’a: aduk lokacin da masoya suke neman juna, idonsu yana rufewa wadda basa ganin waennan abu biyun, amma iyayensu musamman iyayen mata sun kasance suna bincike kan halayya da dabi’ar mijin da yarsu zata aura,wadda hakan abune mai kyau.
A wannan zamani da muke ciki mata sun kasance basa lura da waennan matakai biyun, wadda a duk lokacin da ka hadu da mace da ta kai munzalin aure idan ka tambayeta mijin da take so bai wuce ta ce maka mai kudi kawai takeso ba. Toh shin meyasa mata a wannan zamanin suke son auren namiji mai kudi?
Toh a hiran da mukayi da wasu matasan sun fadi nasu ra’ayin game da wannan batun.
Wata matashiya tace; Da kiyi kuka a kyauyen tsanyawa gara kiyi a Dubai Hajiyata. Mazan ba Allah a ransu.
Wata matashiya rabi; tace Gara a jikaki da kudi kisha wulakanki da ayi miki wulakancin duniya bata dama dakeba.
Wata matashiya mai suna Fatima tace; Kinsan wai hausawa sunce daga na gaba ake hangen nisan ruwa.wasu sunga iyayensu sun sadaukarda soyayyarsu ga iyayensu maza ba domin kudiba amma iyayen maza sunyi ma matan butulci da suka yi arziki, to watakila dalilin kenan da zaisa zakiga yara yanzu sai suce sai mai kudi don ko kin tayashi tara arzikin watace zata zo a baya ta fiki cin arzikin.
Wani matashi mai suna sadik yace; Mata da dama basu son wai su sha wahala a rayuwa ko da fa ace daga gidan marasa hali ta fito, To a irin hakane kuma mazajen suke musu qarya suzo a sunan masu shi amma idan akayi auren kuma zaman yazo ya gagara ayi ta rigingimu.
Sai kuma wani mai suna Muhammad anas yace; mafiya yawan mata dasukeso su auri mai kudi kwadayin abin duniya ne yasa basa duba komai sai kudin, karshe kuma ahau motar kwadayi a kare a tashar wahala.
Kadan daga cikin waenda muka samu muka tattauna dasu kenan game da dalilan dake sa mata son auren namiji mai kudi.
BY: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR