Najeriya kasa ce da ake girmamawa sosai a fadin duniya. Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka fi yawan jama'a a duniya baki daya. Najeriya ta samar da manyan mutane maza da mata tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga kasar Britaniya a shekarar 1960. A yau zamu leka zuwa ga wasu 'yan Najeriya da ke rike da manyan mukamai a duniya.
1. Amina Mohammed
A halin yanzu Hajiya Amina Muhammed tana da shekaru 60 a duniya. A halin yanzu tana rike da babban mukami a Majalisar Dinkin Duniya. Ita ce mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai ci. Ta kuma rike mukamin ministar muhalli a Najeriya.
2. Ngozi Okonjo-Iweala
Madam Ngozi-na daya daga cikin mata masu fada a ji a Tarayyar Najeriya. Ita ce babbar Daraktar Hukumar Kasuwanci ta Duniya a halin yanzu. Ita ce bakar fata ta farko da ta rike wannan mukamin.
3. Akinwumi Adesina
A halin yanzu Akinwumi Adesina yana rike da mukamin shugaban bankin raya kasashen Afirka. Akinwumi Adesina ya kuma taba rike mukamin ministan noma a tarayyar Najeriya. A halin yanzu yana da shekaru 62 a duniya.
4. H.E. Dakta Hajo Sani, OON
Dokta Hajo Sani kwararriya ce ta ilimi kuma manazarci wacce ta shafe shekaru da dama tana gogewa a harkar koyarwa da gudanar da harkokin gwamnati. Ta yi Digiri na farko a fannin Ilimi, Digiri na biyu a fannin Guidance da Counseling da Digiri na uku a fannin Gudanarwa da Nazarin Siyasa. Ta kasance shugabar makaranta na tsawon shekaru goma sha biyu kafin a nada ta a matsayin ministar harkokin mata da ci gaban zamantakewa ta tarayya (1997-98). A lokacin da take rike da mukamin, ta jagoranci wata tawaga zuwa Majalisar Dinkin Duniya (UN) tare da kare rahoton kasa na 2 da na 3 kan CEDAW a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 19 a birnin New York. Dr. Sani ta taba zama Sakatare-Janar na Kungiyar Mata ta Yammacin Afirka (WAWA), reshen Najeriya, daga 2000 – 01.
A shekarar 2021, gwamnatin tarayyar Najeriya ta nada Dr. Hajo Sani a matsayin Jakadiyar Dindindin Dindindin na Najeriya a UNESCO a birnin Paris na kasar Faransa.
By: Firdausi Musa Dantsoho