Abinci yana daga cikin abubuwan da ake bukata na rayuwa.
Dukanmu muna son abinci amma a matsayinmu na ’yan Najeriya, akwai wasu
abincin da ba za mu iya rayuwa ba tare da su ba. Waɗannan abincin sun
riga sun zama wani ɓangare na mu. Ko dai mu dauke su a matsayin karin kumallo,
abincin rana, ko abincin dare. Ko ta yaya, ba za mu iya yin ba tare da
cin su a cikin mako guda ba.
Ga abinci
guda 5 da ba za mu iya rayuwa sai da su ba a najeriya :
1. Biredi: Biredi babban abinci ne a
Najeriya. Ana iya cin sa a kowane lokaci. Ana iya cin shi da wake,
kwai, alale, kosai. Hakanan ana iya cin shi da shayi, kamu, custard, ko
ma abubuwan sha masu laushi. Biredi yana zuwa da girma dama iri
daban-daban kamar burodin agege, burodin sardine, burodin alkama, burodin
cakulat da sauransu.
2. Shinkafa: Shinkafa wata carbohydrate ce da
yawancin 'yan Najeriya ba za su iya rayuwa ba sai da ita. Yana da
ƙankantan adadin calorie kuma yana da kyakkyawan tushen kuzari. Ana iya
dafa shinkafa ta hanyoyi daban-daban. Ana iya dafa shi a matsayin fried
rice, jollof rice, shinkafa kwakwa, farar shinkafa, ko shinkafar ofada.
'Yan Najeriya na iya cin shinkafa kowace rana a kowane lokaci. Ana iya
amfani da shinkafa tare da sunadarai kamar kwai, kifi, nama, da sauran abinci
kamar alala, salad, ko coleslaw.
3. Taliyan Noodles: Babu shakka abinci ne na kowa a
Nijeriya. Ba iya yara ba, har manya suna cin noodles. Noodles yana
da arha, yana kuma da sauƙi da saurin dafawa shi ya sa ake kiransa
da 'noodles na gaggawa watto instant noodles. Ana iya cin Taliyan noodle
da kwai, kifin gwangwani, ko kowane nau'in furotin.
4. Garri: Garri kamar abinci ne mai ceto ga
’yan Najeriya , abinci ne da za ka iya sanya hannunka cikin sauki a lokacin da
ba ka da kudi, kuma ko da kana da kudi, garri abu ne da ba za ka iya yi sai da
shi ba. Gyada, madara, sugar, ruwan sanyi, da garri tabbas hadi ce mai
kyau. Hakanan ana iya amfani da Garri wajen hada Tuwon Eba wanda kuma
abinci ne gama gari ga ’yan Najeriya.
5. Plantain:
Plantain abinci ne mai dadi da yan Najeriya ke so. Ana kuma kiranta ayaba
da ake dafawa. Yana da sauƙi da saurin yin. Ana iya amfani da Plantain
azaman abinci na gefe misali shinkafa da plantain, wake da plantain.
Hakanan za'a iya ba da ita azaman babban abinci misali plantain da miyar kifi.
6. Puff-
Puff watto fanke: shi abun ciye-ciye ne amma abin da 'yan Najeriya ba za su
dauka na kenan. Ana yin shi da soyayyen kwabin flawa ne kuma ana
sayar da shi a gefen hanya. Puff-puff yana da daɗi sosai musamman lokacin
zafi kuma ana iya cinsa tare da lemun kwalba.
Daga: Firdausi Musa
Dantsoho