Thursday 4 March 2021

YADDA AKE HADA MIYAN RIDI

 

Miyan ridi miyace da ake yinta da ridi, kafin yanzu, ba kowa bane yasan cewa ana

amfani da ridi domin ayi miya dashi ba, yawancin mutanenmu na arewa sunfi yin

‘kantu’ dashi. Miyan ridi na da mutukar amfani a jiki kuma anfi yin wannan girkin ne a

jahohin Nasarawa da kuma Neja.

Abubuwan da ake bukata wajen girkin miyan ridi sune;

Ridi

Tattasai,albasa ,attarugu

Ganye (Alaiyahu ko ganyen ugu)

Nama da kifi

Krafish(crayfish)

Manja

Kayan kamshi

Da kuma dunkulen sinadaran dandano

Yadda ake yin miyan ridi.

Dafarko, za a wanke tukunya a dora a wuta, sai a zuba manja cikin tukunyan daidai

gwargwado. A jajjaga attarugu,tattasai, crayfish,da kuma albasa a zuba a cikin

manjan a soya su sama sama sannan a kamanta ruwa a zuba, sai a dauko tafashen

nama da kifi a juye cikin wannan ruwan sai a zuba kayan kamshi da dunkulen

sinadarin dandano , sai koma rufe shi domin abar ruwan miyan ya nuna. Daga nan

sai a dauko garin nikakken ridi wanda aka riga aka niko ta a injin nikan agushi. Sai a

yayyafa mata ruwa a yanka albasa a ta murzata har sai ta kame tadan fara fitar da

mai, sai a bude tukunyan ruwan miyan sai a zuba wannan ridin a cikinta, a wanke

ganyen alaiyyahu ko na ugu a zuba,za a kuma yin anfani da guda biyun,sai a saka

gisihiri daidai misali, a barshi na minti biyar a wuta, shikenan miyan ridin mu ta

nuna. Ana iya cin miyan ridi da tuwon shinkafa, sakwara ,tuwon masara, semovita

harma da tuwon albo.

Maryam Idris.

No comments:

Post a Comment