Kamar
yadda muka samu Daga shafin Sheikh Aminu
Ibrahim Daurawa inda ya fayyace mana dalla dalla wa ya kamata ya yi kayan daki
tsakanin miji da mata. Haka zalika mu ma muka kawo wa masu karatu wannan
bayanin domin karuwan mu gabaki daya.
WA
YA KAMATA YA YI KAYAN ƊAKI?
An daɗe ana ana kai ruwa rana tsakanin
ma'aurata akan waye yake da alhakkin yiwa mace kayan ɗaki? Mijin ta ko ita
amaryar daga cikin sadaƙin ta? ko kuma iyayanta? Ko kuwa dukkan su kowa yana
iya yi? Sannan kayan ɗaki al'ada ne, ko addini? Kyautatawa ne ko dole ne? Bisa
haka muka duba maganganun malamai magabata gamai da wannan batu wanda yaƙi ci
yaƙi cinyewa, kuma a wasu yankuna ya zama kamar wajibi wanda wasu har bashi
suke ɗauka domin su fita kunyar ƴaƴansu, domin kada ya zama abin gori da magana
tsakanin dangi. A wasu al'adu da garuruwa da ƙabilu yin kayan ɗaki haƙƙin miji
ne, wajibi ya tanadi dukkan abinda ake buƙata a gida, kamar shinfiɗa, da
kujeru, da kayan kicin, da dukkan abinda ake buƙata a cikin gida, domin shari'a
cewa tayi miji ya bawa mace wajan zama, ba a ɗora mata yin wani abu ba daga
cikin sadaƙinta, ko iyayanta.
Wasu
al'adu kuma sun ɗorawa amarya da iyayanta yin dukkan kayan gida, abinda miji
zai yi kawai ya tanadi gida amma duk abinda za a saka a gidan ɓangaran mace ne
zasu kawo, shi yasa idan aka sami matsala aure ya mutu, suke zuwa su kwashe
kayansu gaba ɗaya, ko shara ba sa bari. Wasu kuma al'adun suna raba kayan gida
kashi biyu, wani miji ya kawo wani kuma amarya ta kawo, akan haka ne idan an
sami matsalar aure, ake zuwa a tantance kayan miji da na matar, har shari'a
take shigowa kamar yadda mai littafin Tuhfatul Hukkam ya kawo.
FATAWOWIN
MALAMAI AKAN KAYAN ƊAKI AKAN WA YAKE?
Gamai
da maganganun malamai kuwa akan wannan lamari shine mafi yawan malamai kamar
Hanafiyya da Shafiiyyah, da Zahiriyya (Ibn Hazmin), sun tafi akan kayan amfanin
gida akan miji yake. Shi zai tanadi dukkan kayan buƙatu da amfani na gida ba
amarya ba ko iyayan ta, domin tsoran kada a taɓa mata Sadaƙi wajan siyan kayan
(kamar yadda yake faruwa da yawa a cikin hausawa, suna yiwa amarya kayan ɗaki
da sadaƙin ta). Wasu kuma cikin Malaman suna ganin idan iyayan amarya suka yi
kayan ɗakin saboda kyautatawa babu laifi, saboda Hadisin Sayyadina Aliyyu RA
lokacin da ya auri Nana Fatimah RA, Manzon Allah saw ya yi musu kayan ɗaki
(katifah da filo da tukunya) Ibn Majah ya ruwaito. Don haka yin kayan ɗaki
kyautatawa ne ba wajibi bane akan iyaye idan suna da hali su yi daidai
gwargwado, kada a dinga cin bashi ana shiga rigima don yin kayan ɗaki. Mun samu bayyanan nan Daga Shafin Sheikh Aminu
Ibrahim Daurawa Kano.
Rubutawa:
Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment