Shi de warin kafa kamar warin jiki yake domin kuwa yana kunyata mutum a baina jama’a. saboda haka kafafuwan mu suna bukatan kullawa na musamman domin kauracewa warin kafa.
Kowani tafin kafa yana da magudanar zufa 250,000 kuma a kowacce rana yana fitar da zufa kofi mil dari biyar [500ml]. yawan zufa hade da bacteriya kan iya jawo warin kafa.
Warin tafin kafa watto smelly feet a turance matsalan kiwon lafiya ne wadda taruwan yawan zufa dake gina bacteriya a tafin kafa ke haifarwa. Wannan bacteriyan na haifar da tsanannin wari. Haka zalika ko masu tsafta ma, na iya fama da wannan matsalan warin kafan.
Abun burgewa da wannan matsalan warin kafan shine yana da saukin magancewa kuma baya bukatan makudan kudadde wajan magance shi.
Domin hana yaduwan bacteriya da kuma magance matsalan warin kafa, dole a magance matsalan yawan zufa a tafin kafa, saboda haka muka kawo maku hanyoyi mafi sauki wajan kawar da matsalan warin kafa.
1. Yin amfani da sabulu marasa karfi wajan wanke kafan.
2. Shafa spirit a tsakanin yatsun kafa sau biyu zuwa uku a rana yana taimakawa wajan busar da fatan kafan ta yanda bazaiyyi zufa sosai ba.
3. A kaurace wa safan da akayi da kyallin da iska ba zai shiga kafan ba haka zalika a dinga sa takalma da iska zai shiga kafan sosai.
4. A yawaita chanja safan kafa ga masu zuwa makaranta ko yawan son sa safan kafa.
5. A dinga shafawa ko shan antiniotics domin kashe kwayoyin bacteriya da ke taruwa a tafin kafan.
6. Idan har duk abubuwan da muka lissafo basu kawar maku da warin kafa bat oh a tuntubi likita.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment