Gyale bawai kawai kaya bane, ya kasance abun kwalliya na musamman, A arewacin Nigeria gyale ya kasance abu mai muhimmanci cikin siffan fita na kwalliya a kasar hausa.Gyale a wannan zamani ya zarce kayan sawa domin lullube jiki ko hadawa da kaya domin kuwa ya zama abun ado da kwalliya wanda ake yayi, a zamanin da ne ake daukan gyale a matsayin abun da zaa rufe gashin kai kawai kuma ba wani style wanda zai fito da kwalliya, amma a wannan zamanin gyale ya zama abunda zaka iya amfani da ita a bangarori daban daban, zaka iya sanyata da kaya iri iri kama daga atampa, abaya,wando,skirt,haka zalika ana iya sanya gyale zuwa wurare dabandaban.
Haka zalika daurin gyale yana buqatan iyawa domin fitowa tsaf a koda yaushe, haka zalika akwai hanyoyi daban daban na daurin gyale a wannan zamanin, zaka iya yafa gyalen akanka, ko kuma a kafada ko kuma kayi lafiyayyen dauri da shi, shi dai gyale a wannan zamanin yana zuwa iri iri kuma a koda yaushe sake fitowa da sabbin salon gyale akeyi.
A kasan Nigeria a zamanin da ana ganin cewa yan matan arewa ne kawai ke yafa gyale ko daurawa amma a ynxu kasancewanshi abun kwalliya da ado na yayi matan aure ma baa barsu a bay aba wajen ganin sun kawata kwalliyarsu ta hanyan daurawa a kai ko kuma yafawa a kafada musamman da riga da skirt na atampa, haka zalika wasu kabilun sun amsheshi hannu bibbiyu domin bun kasa kwalliya da adonsu na yau da kullum. Abun burgewa da kwalliyar gyale shine zaka iya daura gyale da ko wane irin irin kaya musamman idan ka iya kasha dauri na zamani wadda ake kira da turbans a turance, yawanci zaka ga a wannan zamanin in mace tayi kwalliya na riga da wando tana iya wannan dauri na turban da gyale ta yadda ba sai ta daura wani abu ba sai dai kawai ta yafa bakin abaya nata ta fita,ko kuma ta yi daurin hijab dashi wato raping a turance. Tabbas gyale abin kwalliya ne da amfaninsa baya misaltuwa.
DAGA: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR
No comments:
Post a Comment