Fittaccen mai shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watto Malam Aminu Saira, ya bayyana cewa, idan har ana son a gyara harkokin fina-finai to wajibi ne sai malamai da kuma al’umma sun shigo cikin lamarin domin samun gyaran da ya dace.
Aminu Saira ya bayyana haka
ne a wata tattaunawa da Freedom Radio, yana mai cewa yadda mutane suka yi watsi
da lamarin fina-finan Hausa ne ya sanya a ke samun matsalolin da ake gani a
yanzu a kamfanin.
A cewarsa mai shirya fina finan“Da mahukunta sun shigo cikin
harkokin shirya fina-finai da zuwa yanzu an gyara duk wata barna da ake ganin
ana yi a cikin masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood.”
Rubutawa: Firdausi Musa
Dantsoho
No comments:
Post a Comment