Hazikin mawaki kuma marubucin Arewa Afropop da Afrobeat Ali Jubril Namanjo wanda akafi sanni da suna namenj sun hada kai da mawaki mai tashe hamisu breaker a cikin wata sabuwar waka mai taken DAMA.
Wakan da aka sake ta a ranar juma’a biyar ga watan maris, shekara ta 2021 ya samu karbuwa sosai domin kuwa fitattun jarumai da mawaka sun sanya wakan a shafinsu na yanar gizo.
Haka zalika ayau 8 ga watan maris shekara ta 2021 da rana wakan shine na goma sha takwas a cikin wakoki dake tashe a youtube.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment