Thursday 19 August 2021

KAYATATTUN HOTUNAN BIKIN DINAN CIKA SHEKARU SITIN NA MAI MARTABA MUHAMMAD SUNUSI NA BIYU

 

A ranar goma sha biyar ga watan augusta, shekara ta 2021 ne, kungiyar Nigeria Platform (NP) suka hadawa Mai Martaba Muhammad Sunusi Lamido na biyu liyafan cika shekaru sitin domin nuna masa so, kauna da girmamawa.

Anyi taron liyafan ne a babban dakin taro na International Conference centre dake babban birnin tarrayya Abuja.

Ga hotunan taron bikin:







































By: Firdausi Musa Dantsoho

YADDA AKE HADA LEMUN VIRGIN STRAWBERRY PINA COLADA

 


Wannan lemun haddiyar lemu ce wadda ake hada ta da strawberry,abarba,madaran kwakwa.

Yana da saukin hadawa kuma yana da daddin sha.



ABUBUWAN BUKATA SUNE:

·         Abarba mai kankara

·         Strawberry mai kankara

·         Madaram ruwa

·         Sigar

·         Madaran kwakwa (coconut milk)

·         Lemun zaki

·         Lemun tsami

·         Vanilla extract

·         Kankara (ice cubes)



YADDA AKE HADA LEMUN:

1.       Da farko zamu samu blendan mu mai karfi wadda zai iya markade kankara tabbatar abun markaden mu watto blender in yana da kyau da karfin da zai markade.

2.       Sai mu zuba abarban mu wadda muka yanka kanana yayyi kankara acikin abun markade(blender).            


3.       Zamu dauko strawberry inmu mai kankara mu sa a ciki, sai mu sa lemun tsami, vanilla flavor,sugar, madara, lemun zaki,madaran kwakwa da kankara duk a ciki mu markade.

4.       Bayan mun markade ya markadu toh lemun strawberry pina coladan mu ya hadu.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho

Wednesday 18 August 2021

YADDA AKE HADA CHOCOLATE MILK SHAKE

 


ABUBUWAN BUKATA SUNE:

·         Kankara ( ice cubes)

·         Chocolate ice cream da vanilla ice cream ludayi daddaya

·         Madaran ruwa kofi daya

·         Sigar cokali biyu

·         Coco powder cokali daya

·         Milo  cokali daya



YADDA AKE HADAWA

1.       Da farko zaki yi wa kofinki ado da chocolate syrup kisa a fridge.

2.       A cikin abun markaden ki watto blender ki zuba kankara,ice cream, madaran, ruwa, coco powder, da milo ki markade su gabaki daya.          


3.       Idan ya markadu sai ki fito da kofin ki daga cikin fridge  ki juye a ciki.

4.       Zaki iya kara masa ado da whipping cream idan kina so idan ba kai so toh asha lafiya.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho

OREO MILKSHAKE

 


ABUBUWAN BUKATA SUNE:

·         Kankara

·         Biskit in oreo guda takwas

·         Ice cream ludayi biyu

·         Siga cokali biyu

·         Madaran ruwa kofi daya

 

 


YADDA AKE HADA OREO MILKSHAKE

1.       Zamu zuba  kankara, oreo biskit,ice cream, siga, madaran ruwa sai mu markade su gaba daya.




2.       Bayan ya markadu toh oreo milkshake in mu ya hadu, ga daddi ga sauki.

3.       Asha lafiya

 

By: Firdausi Musa Dantsoho

MATAKAI DA ZA’A BI WAJAN HADA FANKE(PUFF-PUFF)

 


Puff puff sananen abinci ne a kasar Nigeria, wadda yawanci za’a gan ana saidawa a hanya a kasar Nigeria.

Shi puff puff ya kasance abinci mafi saukin samu a hanya da mutum zai iya ci ya kuma koshi.

Ana cinsa ne domin yunwa ko marmari, yana da kuma saukin hadawa idan har mutum yabi matakan da ya dace.



ABUBUWA BUKATA SUNE:

·         Flawa kofi hudu

·         Sikari kofi daya

·         Karamin cokali na yeast

·         Karamin cokali biyu na madaran gari

·         Gishiri kadan

·         Gyadan kamshi

·         Man gyada

·         Ruwa lab lab

 


YADDA AKE HADA PUFF-PUFF

1.       A cikin kwano mai tsafta zamu zuba siga cokali daya  da yeast in mu, sai mu zuba ruwa lab lab rabin kofi a ciki mu juya su hade mu barsh ba minti 10.

2.       Sai kuma a cikin wani kwano mai girma, mu zuba flawan mu kofi hudu, siga kofi daya, madara cokali biyu, gishiri kadan da gyadan kamshi sai mu juya dry ingredients inmu ya hadu.  


3.       Daga nan sai mu dauko hadin yeast inmu mu zuba a ciki muna juyawa muna kara ruwa har mu samu yadda mukeso kar kwabin yayyi tauri kar yayyi ruwa.

4.       Sai mu samu leda da murfi mu rufe kwabin na minti 30 domin ya tashi.                                                            


5.       Bayan minti 30 kwabin mu ya tashi, sai mu daura man mu yayyi zafi.

6.       Idan man mu yayyi zafi sai mu fara jefa kwabin mu na puff-puff a ciki .

7.       Mu kuma tabbata wutan baiyi yawa ba.

8.       Mu soya shi har zai yayi brown gefe biyu . toh fanken mu ya hadu.

 

 

By: Firdausi Musa Dantsoho