Koda wanni bangaren jikin dan adam ne da keda muhimmanci kuma yake taka muhimman rawa a rayuwar mutum. Domin kuwa idan kodar mutum ya samu matsala toh hakan zai iya kashe bangaren jikin mutum, kuma tabbas bada dadewa ba mutum kan iya rasa ransa.
Kodar mutum yana da alhakin shige da ficen abubuwa daga
jikin dan adam. Koda yana taimakawa jikin mutum wajan fitar da abubuwa da jikin
dan adam baya bukata.
Amma akwai wasu matakai da dan adam ya kamata ya dauka
domin kare kodarsa daga samun matsala. Waenan matakan sun danganta da irin
abincin da ya kamata mu daina ci musamman kafin mu kwanta barci.
Wanann haka ne saboda, abinci da aka ci kafin a kwanta
barci bashi da wanni amfani ga jikin dan adam face illa da yake dashi domin
yana gajiyar da koda.
Saboda haka ayau a kiwon lafiya zamu kawo maku bayyanai
akan abinci hudu (4) da ya kamata mu kauracewa cinsu kafin mu kwanta barci
saboda ceto kodar mu da kuma bawa kodar mu ingantaccen kulawa da yake bukata.
1. Soyayyan
abinci: wannan na nufin duk abinci da aka soya kamarsu, soyayyen
dankali,plantain,doya,kaza,kosai da sauransu. Idan har an soya abinci toh
abincin zai kasance da kitse mafi muni da zai kasance a cikin jikin dan adam.
Bayan haifar da cutar koda, shi wannan kitsen yana kawo matsala ga zuciya da
wasu bangaren jikin dan adam.
2. Abincin
gwangwani: waenan sune abincin da ake sa su a cikin gwangwani kamarsu kazan
gwangwani,kifin gwangwani,naman gwangwani da sauransu. Shi wannan nau’in
abincin ya kamata a guji cinsu da dare musamman kafin a kwanta barci. Domin
kuwa yana dauke da chemical wadda yake da illa ga lafiyar kodar mutum.
3. Kayan kwalama: waenan nau’in abincin sune
biskit,plawa, chinchin, meat pie, burger, chocolate, ice cream da sauransu.
Waennan abincin suna takurawa kodar mutum fiye da tunanin musamman idan har aka
ci su kafin a kwanta barci.
4. Barasa:
duk da cewa , barasa ba abinci bane amma ya zama dole mutum ya guji shansa da
dare. Shi barasa yana da matukar illa ga kodar mu kuma yana iya kai mutum ga
kabarinsa idan har ba’a guje masa ba.
A karshe, da fatan zamu kauracewa cin abubuwan da keda
illa ga lafiyan jikin mu, kuma mu dage da cin abinci da ked a inganci ga
lafoyar jikin mu.
By: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment