Wednesday 18 August 2021

MATAKAI DA ZA’A BI WAJAN HADA FANKE(PUFF-PUFF)

 


Puff puff sananen abinci ne a kasar Nigeria, wadda yawanci za’a gan ana saidawa a hanya a kasar Nigeria.

Shi puff puff ya kasance abinci mafi saukin samu a hanya da mutum zai iya ci ya kuma koshi.

Ana cinsa ne domin yunwa ko marmari, yana da kuma saukin hadawa idan har mutum yabi matakan da ya dace.



ABUBUWA BUKATA SUNE:

·         Flawa kofi hudu

·         Sikari kofi daya

·         Karamin cokali na yeast

·         Karamin cokali biyu na madaran gari

·         Gishiri kadan

·         Gyadan kamshi

·         Man gyada

·         Ruwa lab lab

 


YADDA AKE HADA PUFF-PUFF

1.       A cikin kwano mai tsafta zamu zuba siga cokali daya  da yeast in mu, sai mu zuba ruwa lab lab rabin kofi a ciki mu juya su hade mu barsh ba minti 10.

2.       Sai kuma a cikin wani kwano mai girma, mu zuba flawan mu kofi hudu, siga kofi daya, madara cokali biyu, gishiri kadan da gyadan kamshi sai mu juya dry ingredients inmu ya hadu.  


3.       Daga nan sai mu dauko hadin yeast inmu mu zuba a ciki muna juyawa muna kara ruwa har mu samu yadda mukeso kar kwabin yayyi tauri kar yayyi ruwa.

4.       Sai mu samu leda da murfi mu rufe kwabin na minti 30 domin ya tashi.                                                            


5.       Bayan minti 30 kwabin mu ya tashi, sai mu daura man mu yayyi zafi.

6.       Idan man mu yayyi zafi sai mu fara jefa kwabin mu na puff-puff a ciki .

7.       Mu kuma tabbata wutan baiyi yawa ba.

8.       Mu soya shi har zai yayi brown gefe biyu . toh fanken mu ya hadu.

 

 

By: Firdausi Musa Dantsoho

No comments:

Post a Comment