Wednesday 31 March 2021

BABBAN BURINA SHINE NAGA TURAWA SUNA JIN WAKOKIN HAUSA INJI MAWAKI DAN MUSA GOMBE


 

Mawaki mai tasowa dan jihar Gombe Musa Muhammad Dan Musa wadda akafi sanni da Dan Musa ya bayyana babban burinsa a wanni hira da BBC Hausa tayi dashi yayyin da akayi mai tambayoyi game dashi da kuma harkar wakarsa.



Da aka tambayeshi game da burinsa mawakin ya bayyana cewa bashi da wanni buri da ya wuce yaga duk kasashen duniya suna sauraron wakokin hausa, misali har turawa ma, suna jin wakokin hausa kamar yadda muma mu ke jin wakokin wasu yaren da bamu sanni ba, dan haka yake so ace duk duniya suna sauraran wakokin hausa.

Mawakin ya kuma bayyana cewa burinsa na biyu shine ya gan ya zama dan sanda.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

 

 

FITTACCEN JARUMI LAWAN AHMAD YA SAMU KARU DIYA MACE

 


Allah ya albarkaci fittaccen jarumi Lawan Ahmad da iya mace, Lawan Ahmad fittaccen jarumi ne kuma mai shirya shiri ne, wadda aka dadde ana damawa dashi a kamfanin shirya fina finan hausa ta  Kannywood.

Ayau ne fittaccen mai shirya shirin izzar so ya bayyana a shafinsa na Instagram  cewa ya samu karuwa wadda ya sanya hotonsa da jaririyan ya kuma wallafa rubutu kamar haka” Masha Allah hamdan kasiran dayyiban mubarakan, Allah ya azurtani da samun diya mace yau muna kara godiya ga Allah subhahanahu wata’ala, dukansu suna cikin koshin lafiya.

Fitattun jarumai sun taya shi murana tare da yin masa fatan Allah ya raya ta .

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

Monday 29 March 2021

YADDA AKE HADA MIYAR OHA


Miyar oha. (Oha soup).


Miyar oha miya ce da ake Yinta a kudancin Nigeria, can kasan igbo, miyar na da farin jini a nan kasar musammam a bangaren kudancun Nigeria da ma kasashen ketare da suka saba da abincin Nigeria. Miyar nada dadin ci da kuma tarin sinadirai masu amfani a jiki. Inhar kinyi baki daga kudancin kasarmu nuigeria , miyar oha zai dace sosai da abincin karban baki.

Abinda ake bukata wajen hada miyar oha sune ,

Nama

Busashen kifi

Danyan kifi

Ganyen oha, (oha leaves)

 Ogiri

Ganyen uziza (uziza leaves)

Gasashen kifi (smoked fish)

Manja

 Sinadiran dandano

Gwaza (cocoyam)

Attarugu, tattasai,albasa

Krafish

Yadda ake hada wannan miyar oha,

Za a wanke nama a saka tukunya a tafasa tare da kayan kamshi, in naman ta kusa nuna sai a saka wankakken danyen kifi a ciki,tare da busashen kifi da gasashen kifin su nuna tare .

Sai a wanke gwaza a tafasa shi har ya nuna, sai a bare bayan a daka cikin turmi ko kuma a saka a blender har sai ya nika.sai a zuba manja a hada daga nan sai a zuba shi a wancan naman da kifin da yake kan wuta.a barshi yanuna har sai gwazan ya narke cikin ruwan miyan naman.

Sai a dauko wannan ganyen uziza da ganyen oha a yankasu kar yankan suyi kanana sai a wanke da gishiri sosai sannan a zuba a cikin miyan.

Daganan sai a dan motsa shi da cokalin girki a barshi na minti biyar, shikenan miyan oha ya nuna.

Za a iya cin wannan miyan da ko wani irin tuwo, sakwara ,fufu, harda tuwon teba (eba).

Dasga Maryam Idris.

 

Wa Ya Kamata Yayi Kayan Daki Miji Ko Amarya?

 

 


Kamar yadda muka samu Daga shafin  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa inda ya fayyace mana dalla dalla wa ya kamata ya yi kayan daki tsakanin miji da mata. Haka zalika mu ma muka kawo wa masu karatu wannan bayanin domin karuwan mu gabaki daya.



WA YA KAMATA YA YI KAYAN ƊAKI?

 An daɗe ana ana kai ruwa rana tsakanin ma'aurata akan waye yake da alhakkin yiwa mace kayan ɗaki? Mijin ta ko ita amaryar daga cikin sadaƙin ta? ko kuma iyayanta? Ko kuwa dukkan su kowa yana iya yi? Sannan kayan ɗaki al'ada ne, ko addini? Kyautatawa ne ko dole ne? Bisa haka muka duba maganganun malamai magabata gamai da wannan batu wanda yaƙi ci yaƙi cinyewa, kuma a wasu yankuna ya zama kamar wajibi wanda wasu har bashi suke ɗauka domin su fita kunyar ƴaƴansu, domin kada ya zama abin gori da magana tsakanin dangi. A wasu al'adu da garuruwa da ƙabilu yin kayan ɗaki haƙƙin miji ne, wajibi ya tanadi dukkan abinda ake buƙata a gida, kamar shinfiɗa, da kujeru, da kayan kicin, da dukkan abinda ake buƙata a cikin gida, domin shari'a cewa tayi miji ya bawa mace wajan zama, ba a ɗora mata yin wani abu ba daga cikin sadaƙinta, ko iyayanta.



Wasu al'adu kuma sun ɗorawa amarya da iyayanta yin dukkan kayan gida, abinda miji zai yi kawai ya tanadi gida amma duk abinda za a saka a gidan ɓangaran mace ne zasu kawo, shi yasa idan aka sami matsala aure ya mutu, suke zuwa su kwashe kayansu gaba ɗaya, ko shara ba sa bari. Wasu kuma al'adun suna raba kayan gida kashi biyu, wani miji ya kawo wani kuma amarya ta kawo, akan haka ne idan an sami matsalar aure, ake zuwa a tantance kayan miji da na matar, har shari'a take shigowa kamar yadda mai littafin Tuhfatul Hukkam ya kawo.



FATAWOWIN MALAMAI AKAN KAYAN ƊAKI AKAN WA YAKE?

Gamai da maganganun malamai kuwa akan wannan lamari shine mafi yawan malamai kamar Hanafiyya da Shafiiyyah, da Zahiriyya (Ibn Hazmin), sun tafi akan kayan amfanin gida akan miji yake. Shi zai tanadi dukkan kayan buƙatu da amfani na gida ba amarya ba ko iyayan ta, domin tsoran kada a taɓa mata Sadaƙi wajan siyan kayan (kamar yadda yake faruwa da yawa a cikin hausawa, suna yiwa amarya kayan ɗaki da sadaƙin ta). Wasu kuma cikin Malaman suna ganin idan iyayan amarya suka yi kayan ɗakin saboda kyautatawa babu laifi, saboda Hadisin Sayyadina Aliyyu RA lokacin da ya auri Nana Fatimah RA, Manzon Allah saw ya yi musu kayan ɗaki (katifah da filo da tukunya) Ibn Majah ya ruwaito. Don haka yin kayan ɗaki kyautatawa ne ba wajibi bane akan iyaye idan suna da hali su yi daidai gwargwado, kada a dinga cin bashi ana shiga rigima don yin kayan ɗaki.  Mun samu bayyanan nan Daga Shafin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

 

Warin Kafa Da Yadda Za’a Magance Shi [Smelly Feet]

 


Shi de warin kafa kamar warin jiki yake domin kuwa yana kunyata mutum a baina jama’a. saboda haka kafafuwan mu suna bukatan kullawa na musamman domin kauracewa warin kafa.
 
Kowani tafin kafa yana da magudanar zufa 250,000 kuma a kowacce rana yana fitar da zufa kofi mil dari biyar [500ml]. yawan zufa hade da bacteriya kan iya jawo warin kafa.
 

Warin tafin kafa watto smelly feet a turance matsalan kiwon lafiya ne wadda taruwan yawan zufa dake gina bacteriya a tafin kafa ke haifarwa. Wannan  bacteriyan na haifar da tsanannin wari. Haka zalika ko masu tsafta ma, na iya fama da wannan matsalan warin kafan.
 
Abun burgewa da wannan matsalan warin kafan shine yana da saukin magancewa kuma baya bukatan makudan kudadde wajan magance shi.


 
Domin hana yaduwan bacteriya da kuma magance matsalan warin kafa, dole a magance matsalan yawan zufa a tafin kafa, saboda haka muka kawo maku hanyoyi mafi sauki wajan kawar da matsalan warin kafa.
 

1.    Yin amfani da sabulu marasa karfi wajan wanke kafan.
 
2.    Shafa spirit a tsakanin yatsun kafa sau biyu zuwa uku a rana yana taimakawa  wajan busar da fatan kafan ta yanda bazaiyyi zufa sosai ba.
 

3.    A kaurace wa safan da akayi da kyallin da iska ba zai shiga kafan ba haka zalika a dinga sa takalma da iska zai shiga kafan sosai.
 
4.    A yawaita chanja safan kafa ga masu zuwa makaranta ko yawan son sa safan kafa.
 

5.    A dinga shafawa ko shan antiniotics domin kashe kwayoyin bacteriya da ke taruwa a tafin kafan.
 
6.    Idan har duk abubuwan da muka lissafo basu kawar maku da warin kafa bat oh a tuntubi likita.
 
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho
 
 
 

KAYYATATTUN HOTUNA DAGA WAJAN SHAGALIN BIKIN YAR FITTACCIYAR JARUMAR KANNYWOOD HAFSAT BARAUNIYA



Fittacciyar jarumar Kannywood hafsat idris wadda akafi sanni da hafsat barauniya ta aurar da iyarta watto khadija Ibrahim ishaq.

Anyi daurin aure da shagulgulan bikin ne a karshen makon daya gabata,fittattun jarumai da mawaka irin su Ali Nuhu, Mansura Isah, Aisha Humaira, Nazifi Asnanic, Ali Jita, Samira Ahmad, Mama Daso da sauran su  duk sun halarci taron shagalin biki.

Ga kayyatattun hotunan biki

 
















Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

Thursday 25 March 2021

Yusuf Buhari zai angonce da 'yar Sarkin Bichi,

 


Da namiji tilo guda daya ga shugaban kasan nijeriya Muhammadu Buhari watto Yusuf Buhari,  na shirin angwancewa da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Ado Bayero, kamar yadd muka samu rahoto daga Daily Nigerian. Zahra Bayero yanzu haka daliba ce a kasar birtaniya kuma tana  karatun ilmin zanen gine-gine a kasar, yayinda shi Yusuf Buhari ya kammala karatunsa a jami'ar Surrey, Guildford, a Birtaniya. Majiyoyi sun bayyana cewa za'a gudanar da bikin cikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa. "An kaddamar da shirye-shiryen bikin. Kamar da al'ada ta tanada, iyayen mijin sun kai gaisuwa wajen iyayen Zahra," cewar majiyar da aka sakaye sunanta. Majiyar ta kara da cewa da tuni an yi bikin amma saboda rashin kasancewar mahaifiyar Yusuf, hajiya Aisha Buhari, wacce ta dawo daga Dubai inda ta kwashe watanni shida. "Tun da yanzu a dawo ana gab da azumi, lallai za'a yi daurin auren bayan Sallah," majiyar ta kara.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

Wednesday 24 March 2021

YADDA AKE HADA MIYAN KAYAN LAMBU { VEGETABLE SAUCE}

 




Uwar gida  da amarya ku tawo kuji, ba ko da yaushe zaku dinga hada miyan stew ba wasu lokutan a dinga haddawa da miyan kayan lambu wadda a turance ake kiransa da vegetable sauce.

Shi wannan miyan yana da daddin gaske ga saukin hadawa kuma uwargida baya bukatan kashe kudi ga kuma gina jiki.

Kayan lambu na da kyau ga lafiyan jikin dan adam domin yana dauke da sinadirai da ke inganta lafiyan jikin mu, haka zalika, likitoci na yawan bada shawaran a yawaita cin kayan lambu.



ABUBUWAN BUKATA WAJAN HADA WANAN MIYAN SU NE:

*Kaza

*Tumatir

*Albasa mai lawashi

*Karas

*Kabeji

*Dankalin turawa

*Man gyadda

*Jan tattasai

*Koren tattasai

*Gishiri

*Sinadarin daddano

*Thyme


YADDA AKE HADA MIYAN

1.       Ki wanke sai ki yanyanka kayan lambun ki.

2.       Sai ki fere dankalinki ki wanke sai ki yanka shi kananaki markade sh yayyi laushi.

3.       Sai a dauko kazan a yanka, a wanke sai a zuba a cikin tukunya a yanyanka albasa a ciki, a sa sinadarin dandano da thyme, sai a zuba ruwa daidai wanda zai dafa kazan.



4.       Idan da bukata uwar gida zaki iya sa gishiri a tafasan kazan ki. Idan ya dahu sai ki zuba tumatir da kayan lambun ki da man gyadda sai ki rufe ki barshi ya dahu na minti 15.

5.       Sai ki sa karas inki ya dahu na minti biyar.

6.       Bayan minti biyar sai ki zuba nikakke dankalinki da yankakken tattasai da kabeji ki sai ki juya ki rufe ki barshi ya dahu na minti biya.



7.       Toh miyan kayan lambun ki ya hadu, zaki iya cin farar shinkafa ko dafaffen doya ko taliya da wanan miyan.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

 

Tuesday 23 March 2021

JARUMI ADAM A ZANGO YA NEMI TSARI DAGA LUWADI




Fittaccen jarumi, mawaki kuma makidi a kamfanin shirya fina finai ta Kannywood Adam A Zango ya nimi tsari daga niman maza watto luwadi da kuma shiriya ga masu aikatawa.



Adam a zango ya yi hakan ne bayan ya wallafa wanni videon wa’azin Dr Abdullahi Gadon Kaya inda yake bayyanin yadda mumunan dabi’ar neman maza watto luwadi yayyi yawa a tsakanin al’umma da shuwagabanin masu rike da manyan matsayi, har ma da mallamai masu da’awa akan samu masu mummunar dabi’ar a  cewar malamin.



Kamar yadda muka sanni jarumi Adam A Zango tun ba yau ba yake nesanta kansa da irin wannan mummunan dabi’ar neman maza.



A baya ma da zarge zarge suka yi wa jaruman masana’antar kannywood yawa jarumin a wata hirar da akayi da shi da gidan talebijan in liberty ta jihar kaduna a shekara ta 2016 jarumin yayyi ransuwa harda alqur’ani akan cewa bai taba neman maza ba kuma ba’a taba nemansa ba.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho


Monday 22 March 2021

Tayi sujjadar godiya ga Allah bayan da ta gan Ni inji mawaki Nura M Inuwa




Shahharraren mawaki, wadda yayyi fice a kamfanin shirya fina finai ta Kannywood, haka zalika, ya kasance mai dumbim masoya kuma ana ganin wakansa a matsayin nasiha ba,a iya nan ba, wakokinsa ya gyara zamantakewan aure inji wasu  watto mawaki  Nura M Inuwa ya bayyana  yadda wata masoyiyarsa tayi sujjudul shukhur yayyin da tayi ido biyu da shi.

Matashiya wadda Sunan ta  Hafsat ne  amman a yanzu ana kiran ta da Nuriyya saboda tsananin kaunar da take yi wa mawaki Nura M Inuwa.

A ranar Lahadi ne Nuriyya tayi sujjadar godiya ga Allah bayan da aka hada ta da mawaki Nura M Inuwa



Nura M inuwa ya bayyana hakan ne a shafin sada zumuntan sa na facebook,  inda muka samu labarin. Mawakin  ya wallafa rubutu haka yake cewa “

 Hafsa take, amma ana kiranta da Nuriyya dalilin son da take mini,data ganni tayi sujjadar godiya ga ubangiji, ta zubar da hawayen da suka kashen min jiki, a karshe ina rokon Allah ya azurtata da muji nagari.”

Wannan abun yayyi wa masoyan mawakin daddi yayyin da suka ta yabonsa, haka zalika, kamar yadda muka sanni yayyin da wasu ke yabon jarumai wasu kuma na sukar su haka ma ga mawakin wasu sun soke shi gamme da sujjadar da matashiyan tayi.


Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

 

Da mahukunta sun shigo harkokin fina-finai da an gyara duk wata barna a masana’antar inji Aminu Saira

 


Fittaccen mai shirya fina-finan Hausa ta Kannywood  watto Malam Aminu Saira,  ya bayyana cewa, idan har ana son a gyara harkokin fina-finai to wajibi ne sai malamai da kuma al’umma sun shigo cikin lamarin domin samun gyaran da ya dace.



Aminu Saira ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Freedom Radio, yana mai cewa yadda mutane suka yi watsi da lamarin fina-finan Hausa ne ya sanya a ke samun matsalolin da ake gani a yanzu a kamfanin.



A cewarsa mai shirya fina finan“Da mahukunta sun shigo cikin harkokin shirya fina-finai da zuwa yanzu an gyara duk wata barna da ake ganin ana yi a cikin masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood.”

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

Thursday 18 March 2021

TITTLE: GYALE ABUN KWALLIYA NA ZAMANI A KASAR NIGERIA

Gyale bawai kawai kaya bane, ya kasance abun kwalliya na musamman, A arewacin Nigeria gyale ya kasance abu mai muhimmanci cikin siffan fita na kwalliya a kasar hausa.Gyale a wannan zamani ya zarce kayan sawa domin lullube jiki ko hadawa da kaya domin kuwa ya zama abun ado da kwalliya wanda ake yayi, a zamanin da ne ake daukan gyale a matsayin abun da zaa rufe gashin kai kawai kuma ba wani style wanda zai fito da kwalliya, amma a wannan zamanin gyale ya zama abunda zaka iya amfani da ita a bangarori daban daban, zaka iya sanyata da kaya iri iri kama daga atampa, abaya,wando,skirt,haka zalika ana iya sanya gyale zuwa wurare dabandaban.

Haka zalika daurin gyale yana buqatan iyawa domin fitowa tsaf a koda yaushe, haka zalika akwai hanyoyi daban daban na daurin gyale a wannan zamanin, zaka iya yafa gyalen akanka, ko kuma a kafada ko kuma kayi lafiyayyen dauri da shi, shi dai gyale a wannan zamanin yana zuwa iri iri kuma a koda yaushe sake fitowa da sabbin salon gyale akeyi.

A kasan Nigeria a zamanin da ana ganin cewa yan matan arewa ne kawai ke yafa gyale ko daurawa amma a ynxu kasancewanshi abun kwalliya da ado na yayi  matan aure ma baa barsu a bay aba wajen ganin sun kawata kwalliyarsu ta hanyan daurawa a kai ko kuma yafawa a kafada musamman da riga da skirt na atampa, haka zalika wasu kabilun sun amsheshi hannu bibbiyu domin bun kasa kwalliya da adonsu na yau da kullum. Abun burgewa da kwalliyar gyale shine zaka iya daura gyale da ko wane irin irin kaya musamman idan ka iya kasha dauri na zamani wadda ake kira da turbans a turance,  yawanci zaka ga a wannan zamanin in mace tayi kwalliya na riga da wando tana iya wannan dauri na turban da gyale ta yadda ba sai ta daura wani abu ba sai dai kawai ta yafa bakin abaya nata ta fita,ko kuma ta yi daurin hijab dashi wato raping a turance.  Tabbas gyale abin kwalliya ne da amfaninsa baya misaltuwa.

DAGA: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR 


TITTLE:AMFANIN MADARAN WAKEN SUYA GA LAFIYAR DAN ADAM


Madaran waken suya na daya daga cikin hanyoyin da akafi sani na kiwon lafiya masu gina jiki,waken suya na dauke da wasu sinadarai wanda keda matukar muhimmanci ga lafiyar dan Adam.babban abun ciki shine protein da kuma vitamin.

Waken suya na daya daga cikin abinci marasa illa,muddin bakada lahani ga waken suya zaka iya shan madararsa, shan karamar kofi 1 na madaran waken suya a kowace rana babban hanya ne na samun wasu fa'idodin lafiyarka. 

Maganin da madaran waken suya keyi sun hada da: 

Maganin ciwon kwakwalwa:

Madaran waken suya na iya taimakawa wajen rage hadarin dake kai domin yana kunshe da maganin kananan kwayoyin cuta tare da fa'idodin lafiyar kwakwalwa. Madarar waken suya na iya taimakawa wajen hanawa da magance rikicewar yanayin damuwa.

Rigakafin ciwon kansa:

Kamar yadda calcium ke taimakawa wajen rage hana cututtukan kansan hanji haka zalika madaran waken suya na taimakawa wajen rigakafin cutar kansa , yana taimakawa wajen kawarda cututtukan da ke haifar da cutar kansa daga jikin dan Adam.

Ciwon zuciya:

Cutar zuciya itace babbar matsalar lafiyar maza, ana shawartan maza da su ci abinci mara nauyi mai kyau da protein don hana matsalolin zuciya da jijiyoyin jini, kofi daya na madaran waken suya ya kunshi protein, kuzari da kuma wadataccen mai. Haka zalika madaran waken suya na inganta lafiyar jini da matakan cholesterol. 

DAGA:UMMU-KHULTHUM ABDULKADIR 



Wednesday 17 March 2021

ALLAH YAYYI WA RABI’ATU HARUN MATAR DA TAYI WAKAR ‘MAI DARAJA ANNABI MA’AIKI RASUWA

 


Fitacciyar mai wakokin yabon annabi sayyada Rabi’atu Harun ta rigamu gidan gaskiya,ta rasu ne a jiya talata 16 ga watan maris shekara ta 2021 a rigasa kaduna.

Mijin marigayyiyan sharif mu’az ne ya tabbatar da rasuwarta yayyin da ya bayyana cewa ta rasu ne bayan jinya na makonni uku, ya kara da cewa  mutuwarta ta girgiza shi ya bayyana matarsa a matsayin mace mai hali nagari ya kara da yin mata addu’ar Allah ya jikanta da rahama.



Marigayyiyan ta yi wakokin yabon manzon Allah masu tarin yawa ciki akwai mai daraja annabi ma’aiki, zahra’u fadima,shukriyya sajida da sauransu masu son wakokinta sunyi jimamamin rasuwarta tare da yin mata adu’an Allah ya jikanta ya gafarta mata.

Ta rasu ta bar mijinta da ya’ya biyu a duniya, allah ya jikanta da rahama amin.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho