Kilishi wadda ake kira beef jerky a turance nama ne da ake sarafa shi a yankin Hausawa a Arewacin kasar Najeriya, ko Arewacin lardin Kamaru, ko a yankin Jamhoriyar Nijar. Ana hadda kilishi ne dai da naman shanu, ko rago, ko akuya, ko na rakumi. Masanan sarafa kilishi sun bayyana shi da zabebben nama wanda sai asalin mahauci dan gado ke yin shi. Mafi shaharar kilishi dai da naman shanu ake yin shi.
ABUBUWAN BUKATA SUNE:
· Tsokan
nama
· Sinadarin
dandano
· Garin
kuli kuli
· Gishiri
· Garin
yaji
· Kanumfari
· Citta
· Tafarnuwa
· Masoro
· Albasa
· Soyyayyen gyada
YADDA AKE HADDA KILISHI
1. Da
farko zamu fara da fere naman mu.
2. Bayan
mun fere, sai mu shanya shi naman ya bushe, hakan na iya daukan kwana biyar
zuwa goma amma, idan kina da oven sai kiyi anfani da shi wajan busar da naman
ki on low heat.
3. Bayan
naman ya bushe sai mu dauko su kayan haddin mu, su kayan dandano da kamshi, mu
kwabasu guri daya da dan ruwa kar yayyi ruwa sosai kuma kar yayyi kauri.
4. Daga nan sai mu dauko bushashiyar naman mu mu gaurayya cikin haddin, sai mu maida naman rana ko cikin oven domin ya bushe, kuma haddin ya shiga cikin naman sosai.
5. Idan
har a oven kika sa naman ki toh kilishin ki ya hadu, in kuma a rana ne toh dole
ki gasa kilishin ki a wuta domin kayan hadinki ya shiga ciki Sosai.
6. Bayan kin gasa toh kilishin ki ya hadu.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment