Amarya, uwargida kina fuskantan matsala wajan hadda faten wake? Toh wannan naki ne zamu koya maku yadda ake hadda faten wake hadadde.
Shi faten wake abinci ne da ake ci a kowani bangare a kasar nijeriya, ana cin sa da agada watto plantain, ana cinsa da garrin kwaki,da bredi dama koko.
Ana amfani da farin wake ko jan wake wajan hada wannan faten.
ABUBUWAN BUKATA SUNE:
· Wake
· Man ja
· Tumatir
· Tattasai
· Attarugu
· Albasa
· Cray fish nikakke
· Sinadarin dandano da gishiri
YADDA AKE HADAWA
1. Zamu wanke waken mu sai mu zuba a tukunya mu zuba ruwa yafi waken yawa.
2.
Mu dafa waken har sai ya dahu yayyi laushi,
hakan na daukan minti arba’in zuwa awa daya.
3. Yayyin da waken mu ke dahuwa, mu markade tumatir, attarugu, tattasai da albasan mu, mu aje a gefe.
4. Bayan waken mu yayyi laushi ya dahu sai mu zuba su markadaden tumatir in mu a cikin waken akan wutan mu kuma rage zafin wutan zuwa low.
5. Sai mu bar waken da tumatir in ya dan dahu na minti goma, sai mu zuba crayfish, sinadarin dadano, gishiri da man ja a juya sai a kuma barinsa ya dahu na minti goma.
6. Bayan minti goma faten waken mu ya hadu.
Rubutawa:Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment