Fittaccen darakta a kamfanin shirya fina-finan hausa ta Kannywood Hassan Giggs da matarsa tsohuwar jarumar Kannywood Muhibbat Abdulsalam sun cika shekaru goma sha uku cif da aure.
Daraktan da matarsa sun kasance cikin jaruman Kannywood da suka
aura juna, kuma auren yayyi karko, banda haka sun kasance ma’aurata masu son
ganin cigaban juna da kuma taimakawa juna.
Hassan Giggs da muhibbat cike da farin ciki, sun sanar cikan su
shekaru goma sha uku da aure a shafinsu
na Instagram.
Darakta Hassan ya fara da godiya ga Allah (S.W.T) ubangijin
talikai sama da kasa, dan adam da aljannu da mala’iku da komai da komai daya
nuna masu shekara goma sha ukku 13 da aure.
Ya kuma gode wa ubangiji da ya hada shi da kyakyawan matarsa,kuma
uwar kyawawan iyayansa Humaira,Azeema da khadija.
Itama muhibbat kamar yadda ta wallafa a shafinta ta fara ne da
godiya ga ubangiji,tare da bayyana cewa yau auren su shekaru goma sha uku tare
da Hassan Giggs, sa’annan tayi fatan Allah ya kara masu so da kaunar juna ya
raya masu zuri’an su ya kuma sa Hassan ne mijinta a aljanna.
Manajan Tozali da ma’aikatan
ta na tayasu murna tare da yin masu fatan alkhairy.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment