Jaruma wadda mabiyanta a shafin Instagram suka kai miliyan daya, yayin da ba,a samun jarumai mata masu shekarunta da irin wannan adadi .
Fitacciyar
jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood da ke arewacin Najeriya, Saratu Gidado
wacce aka fi sani da Daso, ta ce wani lokacin da gangan ‘yan fim ke tada kura a
shafukan yanar gizo wadda zai janyo hankalin jama’a zuwa kansu.
Daso ta bayyana hakan
ne a wanni hira na musamman da muryar amurka sukayi da ita.
Ga abun da ta fada kamar “Kin
san mu ‘yan fim kamar ‘yan siyasa muke, idan mun ga dama za mu rikita duniyar
gaba daya ido ya dawo kanmu, wato idan mun ji rayuwar ta dan lafa muna so mu
motsa ta.” Daso ta ce.
Jarumar
wacce ta ke fitowa yawanci a matsayin mai barkwanci, ta bayyana hakan ne a lokacin
da akayi mata tambaya kan wani bidiyo da ta wallafa a shafin Instagram inda aka
ganta tana wanka a wurin waka na swimming pool.
Daso ta kara da cewa da gangan tayi kuma Sai da ta kaikaici Lahadi babu kowa,
ta je ta biya kudi, ta yi wanka ita kadai sai kanwata da ta yi mata bidiyo.
Ta kuma ce “Alhadulillahi! mabiya miliyan daya da ta samu a
Instagram, baiwa ce daga Allah. Kafin ta yi da yawa sun yi, wasu suna da fiye
da miliyan daya.”
Ta kara da
cewa, “abin da ya sa abin ya zama babba a idon jama’a, shi ne, saboda ganin ita
dattijuwa ce kuma matar aure, shi ya sa ake cewa ya aka yi haka?
Fim na
baya-bayan nan da jarumar take taka rawa a ciki shi ne, fim din “Gidan Danja,”
wanda fim ne mai dogon zango.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment