Ni da
Mata ta duk mun yi fushi da juna. Daga yanayin fuskata, matata ta san
cewa na shirya sosai don ci gaba da rashin Magana da ita a safiyar wannan
ranan. Ita ma ta fusata bata damu da yin mun magana ba.
Na
fita daga gidan sai itama ta kulle kofa ta biyo ni a baya. Tun da ba mota
muke da ba, ko da yaushe muna shiga bas ɗaya don tafiya wajan aiki kowace
safiya kuma muna tabbatar da cewa mun zaune tare da juna a bas ɗin.
Zan
sauke a Manda hill ita kuma za ta sauke a zesco.
Amma
yau bana son zama kusa da ita Saboda Ina fushi da ita. Haka na zauna a
kujerar baya ita kuma ta zauna a gaba, kusa da wani kyakkyawan dan sanda .
Mutumin
ya kalli mata ta. Na ga yadda yake kallon fuskar ta cike da
sha'awa. Sannan yace mata tayi kyau. Mata ta ta yi murmushi ta ce
masa na gode.
Ya
tambayi mata ta ina za ta, sai ta ce masa za ta je aiki.
Duk
wannan ina zaune a baya ina sauraron hirarsu.
"Sunana
Mwansa Mweemba. Ni dan sanda ne kamar yadda kika gani a cikin kayan da nasa. An
tura ni Lusaka wata guda da ya wuce. A yanzu haka ina kan hanyar zuwa wurin
aiki."
Mata
ta ta gyada kai. Da conductor ya nemi mata ta ta biya kuɗin mota, jami’in ya ce
zai biya, ya ciro kudi ya ce kudin motan su biyu.
Mata
ta ta yi masa godiya ta yi murmushi.
Sai
Dan sandan ya ci gaba da magana.
"Don
haka nan ba da jimawa ba zan sauka a Munali an saukar da ni a sansanin 'yan
sanda na Chelston, ban sani ba ko za ki iya zuwa gaishe ni wata rana? Zan iya
samun lambar wayarki?"
Ban
ɓata lokaci ba a gurguje na taba mata ta a kafadarta nan da nan.
Ta
juya.
Sai
na tambaye ta.
"Da
fatan kin tuna kin saka cokali a cikin akwatin abincin ranan Kasubas? Kin san
kullum kina mantawa."
Mata ta
ta yi mamaki sosai. Wata kila tana tunanin ko wacece Kasuba, me yasa na
za6i magana da ita. Kafin ta fara yin mun wasu tambayoyi na kara da cewa.
"Kiyi
qoqarin ki dauke ta daga makaranta, yau zan dawo gida a makare, ki dafa min
ifinkubala in na dawo zan ci abinci kafin na kwanta."
Mata
ta ta rikice.
Sannan
ta kalli dan sandan ta mayar da kallonta gareni. Ta fahimci abin da nake
ƙoƙarin yi.
"Toh
honey." Ta gyada kai.
Dan
sandan ya juyo ya Kalle ni. Ya gaishe ni. Sai ya tambayi mata ta.
"mijinki
kenan?"
Mata
ta ta gyada kai. Dan sandan ya dinga kallo na akai-akai.
Sannan
ya kalleni na karshe yayi mun murmushi.
Ban
yi masa murmushi.
Da
muka isa Chainama na sauko daga motar, na ja mata ta tare da ni.
Mata
ta ta kasa daina dariya. Yayin da muke shirin shiga wata bas, sai ta
tambaye ni.
"Honey
waye Kasuba?"
"Kasuba
diyar mu ce da zamu haifa nan gaba. Shiga bas mu tafi."
Mata
ta tayi dariya.
Muka
shiga wata bas a wannan karon, mun zauna tare da juna ne a cikin bas in.
Kuma a wannan karon ni na biya mata kudin mota.
Lokacin
da kuka bawa abokin tarayyan ku tazara, ta jiki koh zuciya, Toh kun bar
shaidan ya mamaye wannan gurbin kenan. Ya ɗauki matsayinka ba tare da
izininka ba kuma ya gina wa kansa gida a madadinka. Kada ku bar shaidan
ya sami wuri a gidanku. Ku rufe duk wata gibi dake tsakanin ku.
Ku
Sanarwa Junan ku cewa zaku kasance tare. Ubangiji Allah ya albarkaci dukan
aure.
Daga:
Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment