A yayin da jaruman Kannywood ke ci gaba da fuskantar kalubalen
sana’a da zamantakewar al’umma a muhallinsu, wasu ‘yan wasan kwaikwayo mata sun
tsunduma cikin cece-kuce a tsawon shekaru nan.
Daga cikin irin wadannan al’amura na baya-bayan nan har da cece-kucen da
ya biyo bayan wata magana da fitacciyar jaruma Nafisa Abdullahi ta yi game da
iyaye su daina haihuwan yayan da bazasu iya kula dasu ba. Baya ga Nafisat
Abdullahi , Akwai wasu ’yan fim guda hudu na Kannywood da suka janyo cece kuce
a shafukan yanar gizo .
A ranar 16 ga Afrilu, Nafisat ta wallafa a shafinta na Tuwita, "Ku daina haihuwa yayam da baza ku iya kula da su ba.
Wallafar Tweeta din ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, daga
wasu 'yan arewacin Najeriya da suka fassara shi da cewa kira ne da ya sabawa
tsarin ilimin Alkur'ani da aka fi sani da "Almajiranci", yayin da
wasu ke ganin ba ta da 'yancin da za ta magance matsalar zamantakewar al'umma.
kasancewarta yar wasan kwaikwayo.
Nafisa ta dage cewa matsalar ba ta shafi ta ko wasu masu gata ba amma
ga yara masu tasowa da iyayensu ke turasu zuwa tituna da sunan karatun
Alkur’ani.
Rahma Sadau
Za’a iya kwatanta Rahama Sadau a matsayin jarumar da ta fi kowa janyo cece-ku-ce, a Kannywood wadda ta ke tattare da labaran cece kuce biyo bayan sana’arta a matsayin jaruma.
A shekarar 2016, an dakatar da ita daga yin wasan kwaikwayo a Kannywood
saboda fitowar ta a wani faifan bidiyo na waka inda aka gan ta tana rungume da
mawakin Najeriya, Classiq. Daga karshe dai an yafe mata sannan ta koma wasan
kwaikwayo.
Jarumar ‘yar asalin jihar Kaduna da ke fitowa a fina-finan Kannywood da
na Nollywood, ta kuma haifar da zazzafar cece-kuce a shafukan sada zumunta kan
wasu hotuna da ta wallafa a shafukanta na Instagram da Twitter a shekarar 2020.
Hotunan dai sun janyo cece kuce Inda har ya janyo batanci Ga manzon Allah hakan
ya kasance cin mutunci ga musulman arewacin Najeriya. al'amarin da ya sa daga
baya ta nemi gafara ta cire hotunan.
Sadiya Haruna
Sadiya Haruna wata jarumar fina-finan Kannywood ce da ta yi ta janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta kan yadda ta wallafa hotunanta da bidiyon tsiraicin da yawancin masoyanta ke ganin ba su dace ba.
A watan Fabrairu ne wata kotun majistare ta Kano ta yanke wa jarumar hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida ba tare da zabin tara ba saboda bata sunan wani abokin aikinsu, jarumi Isa A. Isa.
Ana tuhumar jarumar da bata sunan Isa a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta.
Fati slow
Jarumar Kannywood, Fati Usman, wacce aka fi sani da Fati Slow a kwanakin baya ta kasance abin ban dariya da cece-kuce a shafukan sada zumunta tsakanin 'yan arewacin Najeriya.
A cikin watan Fabrairu ne ta shiga takaddama da fitaccen mawakin Hausa,
Naziru Sarkin Waka, kan wani faifan bidiyo na TikTok da ta yi tana kiransa da
mazinaci (a matsayin martani ga ikirari da mawakin ya yi na cewa wasu ’yan fim
na neman yin lalata da ’yan fim mata kafin a raba musu matsayi a fim). Daga
baya da ya bata kyautan naira miliyan 1 ta ce ta yi nadamar wannan zargi
kuma ta nemi gafararsa.
Hadiza Gabon
Anyi cece kuce a shafukan sada zumunta yayin da a shekarar 2019 aka ga fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Gabon, tana cin zarafin wata jaruma Amina Amal a wani hoton bidiyo na Instagram.
Gabon dai ta yi ikirarin cewa Amal na zarginta da kasancewa 'yar madigo
wanda hakan ya sa ta fusata ta dauki wani faifan bidiyo tana dukan Amal,
lamarin da ya tilasta mata ta amsa zargin karya ne.
Bidiyon ya harzukar da mutani dama daga cikin mabiyan jaruman biyu,
lamarin da ya sa wasu kungiyoyi suka yi barazanar kai karar Gabon saboda cin
zarafi. An dai ce wasu masu ruwa da tsaki a harkar masana’antar ne suka sasanta
‘yan fim din biyu
Daga: Firdausi Musa Dabtsoho
No comments:
Post a Comment