Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara tantance masu neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Ana gudanar da atisayen ne a asirce a wani
shahararren otel dake Abuja, babban birnin tarayya (FCT).
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi
Adamu; Tuni dai sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore, da sauran
jiga-jigan jam’iyyar suka isa wurin da za a gudanar da atisayen, kamar yadda
gidan talabijin in Channels ya tabbatar.
Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma dan majalisa mai
wakiltar yankin Ogun ta tsakiya, Sanata Ibikunle Amosun, wanda kuma ke neman
tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC na cikin wadanda suka
isa wurin da za a gudanar da atisayen.
A halin da ake ciki, wata majiya ta shaida wa
gidan talabijin na Channels cewa kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar
APC na karkashin jagorancin Mista John Oyegun, tsohon gwamnan jihar Edo ne kuma
tsohon shugaban jam’iyyar na kasa.
Fiye da mambobin jam’iyyar 20 da suka hada da
ministocin shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisa, da ‘yan kasuwa, da dai
sauran su, sun karbi fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da kuma
nuna sha’awarsu a kan Naira miliyan 100.
Yayin da masu neman shugabancin kasar suka biya
wa kansu kudaden fom a wasu lokuta, kungiyoyi daban-daban sun sayi tikitin
tsayawa takara ga wadanda suka fi so - matakin da wasu daga cikin wadanda suka
amfana suka yi watsi da shi.
Daga cikin wadanda suka fito fili suka ki
amincewa tiketin takarar jam’iyyar APC da aka siya musu sun
hada da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma shugaban bankin ci gaban
Afirka (AfDB), Dr Akinwumi Adesina.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment