Tuesday, 31 May 2022

Dalilin Da Yasa Tambuwal Ya Sauka Wa Atiku inji Kakakin tambuwal





Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Tambuwal (TCO), Prince Daniel, ya bayyana dalilin da ya sa Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya ajiye mukaminsa ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka kammala a ranar Asabar da ta gabata.

Atiku ya lashe zaben ne da kuri’u 371 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, wanda ya samu kuri’u 237 bayan Tambuwal ya janye wa Atiku.

Kakakin ya ce Tambuwal ya sauka ne sakamakon kishin kasa da yake nuna wa ci gaban Najeriya.

 

Sanarwar ta kara da cewa; “Mai Girma Gwamnan Jihar Sakkwato Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, CFR na taya tsohon mataimakin shugaban kasa Alh. Atiku Abubakar, GCON a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP a zaben fidda gwanin da aka kammala.

“Gov. Tabuwal ya yanke shawarar janyewa daga takarar duk da cewa ya fi son ya ci tikitin ne saboda tsananin kaunar Najeriya da jam’iyyar musamman.

“Ga dimbin magoya bayanmu muna so ku sani cewa mun dauki wannan matakin ne dan kishin kasa, inda muka sanya kasarmu Najeriya da jam’iyyarmu ta PDP gaba da burinmu na kashin kai wanda muka sake nanata cewa bai kai muradin kasa ba.”

“Duk da haka, domin tabbatar da samun nasara a zaben yayin da PDP ke shirin kayar da APC a zabe mai zuwa na Fabrairu 2023, ya bukaci Wazirin Adamawa da su gudanar da yakin neman zabe wanda zai hada kan jam’iyyar da kasa baki daya.

“Mai martaba ya kuma yi matukar godiya ga shugaban kwamitin yakin neman zabensa bisa jagoranci nagari, da daukacin tawagar da dukkan wakilansa da kuma dumbin magoya bayansa a fadin kasar nan kan irin goyon bayan da suka bayar kafin taron da kuma bayan taron.

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho

 



Monday, 30 May 2022

Harin Jirgin Kasa: Kuna Iya Sauraron Waɗanda Akayi Garkuwa Da Ko kuma Ku Yi Watsi Da Su, In ji ɗan Ta'adda Ga Gwamnatin Taraiyya

 

 


Daya daga cikin ‘yan ta’addan da suka kama fasinjojin jirgin kasa da
aka kai wa hari a Kaduna ranar 28 ga watan Maris, ya ce gwamnatin 
tarayya na da zabin sauraron wadanda abin ya shafa ko kuma 
ta yi watsi da su.

Dan ta’addan da ya rufe fuska ya yi magana a wani sabon faifan bidiyo inda takwas daga cikin wadanda abin ya shafa – mata uku da maza biyar – suka roki Gwamnatin Tarayya ta taimaka.

 

Mutumin da ya yi magana da turanci ya ce, “Mu ne mutanen da suka yi awon gaba da wadannan mutane daga jirgin Abuja zuwa Kaduna, don haka suna kira gare mu cewa suna son tattaunawa da gwamnatin tarayya, kuma mun ba su damar yin magana. Ya rage a gare ku ku saurare su ko ku yi watsi da su.”

 

Wata da aka kama, mai suna Mariam Abubakar, ta ce ‘ya’yanta sun yi rashin lafiya a hannunsu.

 

“Ina daya daga cikin wadanda aka kama a cikin jirgin tare da ’ya’yana hudu da mijina. Muna kira ga gwamnatin tarayya, iyalanmu da duk wanda zai iya don Allah a kawo mana agaji. Mun kasance a nan har tsawon kwanaki 62 kuma yanayin rayuwa mara kyau wanda ba a iya misaltawa.

 

“Mun yi rashin lafiya. Hasali ma, daya daga cikin ’ya’yana, biyu daga cikinsu ma ba su da lafiya a halin yanzu ba su da magunguna. Don haka muna rokonku da ku kawo mana agaji,” inji ta.

 

‘Yan uwan ​​wadanda abin ya shafa dai sun yi ta kiraye-kirayen a sake su, inda gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin daukar matakin ceto fasinjojin.

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho

 

 

Kotu ta bawa EFCC umarnin tsare Okorocha bisa zargin almundahanar N2.9bn

 


Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha a hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC har sai an yanke shawarar neman belinsa.

Wadda za’a tsare tare da Okorocha a hannun EFCC, jigo ne a jam’iyyar APC, kuma aminin tsohon gwamna, Anyim Nyerere Chinenye.



Mai shari’a Inyang Ekwo ya ba da umarnin ne a ranar Litinin bayan da Okorocha, Chinenye da kamfanoni biyar suka gurfana a gaban kuliya bisa zarge zarge 17 na halasta kudaden haram da EFCC ta shigar.

Mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraren karar Okorocha da Chinenye har zuwa ranar Talata.

Kamfanoni biyar sune: Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited da Legend World Concepts Limited.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho

 

 

 



APC ta fara tantance 'yan takarar shugaban kasa gabanin zaben fidda gwani

 

 


Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara tantance masu neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.

 Ana gudanar da atisayen ne a asirce a wani shahararren otel dake Abuja, babban birnin tarayya (FCT).

 Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu; Tuni dai sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore, da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka isa wurin da za a gudanar da atisayen, kamar yadda gidan talabijin in Channels ya tabbatar.

 Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma dan majalisa mai wakiltar yankin Ogun ta tsakiya, Sanata Ibikunle Amosun, wanda kuma ke neman tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC na cikin wadanda suka isa wurin da za a gudanar da atisayen.

 A halin da ake ciki, wata majiya ta shaida wa gidan talabijin na Channels cewa kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar APC na karkashin jagorancin Mista John Oyegun, tsohon gwamnan jihar Edo ne kuma tsohon shugaban jam’iyyar na kasa.

 Fiye da mambobin jam’iyyar 20 da suka hada da ministocin shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisa, da ‘yan kasuwa, da dai sauran su, sun karbi fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da kuma nuna sha’awarsu a kan Naira miliyan 100.

 Yayin da masu neman shugabancin kasar suka biya wa kansu kudaden fom a wasu lokuta, kungiyoyi daban-daban sun sayi tikitin tsayawa takara ga wadanda suka fi so - matakin da wasu daga cikin wadanda suka amfana suka yi watsi da shi.

 Daga cikin wadanda suka fito fili suka ki amincewa tiketin takarar jam’iyyar APC da aka siya musu sun hada da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma shugaban bankin ci gaban Afirka (AfDB), Dr Akinwumi Adesina.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho

 

 

APC's bitter but puissant pill.

 


 

By Tahir Ibrahim Tahir Talban Bauchi. 

 

Deep down, as an APC faithful, I have harbored a genuine fear of having to contend with an 'ATIKU', as the flagbearer of the PDP in the 2023 polls. The man is a sagacious politician, a ballot veteran and a professional linguist of the Nigerian language and mentality. Woe betide you, if you dare underestimate his political prowess and war-chest. The legendary 12 million vote’s man, PMB, narrowly escaped Atiku's onslaught at the ballot, in the 2019 general elections, and many believed that, had the elections not been postponed, he would have won. His continued attempts at the Presidency for over 30 years, have made him a veteran and master-strategist at the polls. One can never tell; but he just might finally clinch it this time -- if the APC does not take good care. 

 

        The younger, vibrant, robust and more technocratic aspirants have all been floored or edged out of the PDP primaries. One of them withdrew and surrendered his huge support-votes that finally tilted the race in Atiku's favor. PDP has actually presented its most formidable candidate in the last 24 years, since OBJ of 1999. The APC, morphing through different party names over the same period, had PMB as their best. Atiku rightly takes over from OBJ, as the next finest, from the PDP hightable. The APC has a similar array of the younger and vibrant stock of aspirants, just as those of the PDP. The huge poser here is, can they match or tackle Atiku? Do they have the spread, the wings and the flight time? Can they safely land to a thunderous ovation by their passengers as they pilot their parties to victory? Are they his mates politically?

 


           There is only one aspirant in the APC shed that can match Atiku, and even surpass him, in as far as talking politics, and election victory are concerned. Aside the base, the spread, the political might both in strategy and resources; Tinubu is light years ahead of Atiku, in terms of achievements, and dividends of a life long political struggle. Tinubu was once the rallying point of all pro-democracy activism against the military, back in the 90s. Tinubu succeeded in pulling the rug from under the PDP in the South West, when it was at its strongest hour. Tinubu is the father of the IGR drives and templates that are being replicated across the country, from a Lagos model/ prototype. Tinubu's school of politics has the best professors in the country today, and is still graduating world class surgeons, engineers and barristers. Tinubu's sacrifices politically, outclass that of any other politician worth his salt nationally. Almost single handedly building parties and party structures from scratch, is no mean feat and hardly can his rivals boast of the same achievement. 

 


        APC must honor its unwritten agreement of power shift, in the spirit of federal character and rotation. Tinubu as a southerner, is the only politician that has exhibited the Northern brand of inclusiveness in politics. A former Northern governor and serving Senator, Kashim Shettima of Borno, is leading his campaigns. An honorable member from Kebbi state, Aminu Suleiman bought his forms for him and is mobilising groups for him across the North. Three quarters of the National Assembly are rooting for him. Quite a number of the Northern governors have his support and a huge chunk of the delegates voting in the primaries, especially those from Kano, are already in his corner. 

 

        We all observed the PDP Presidential primaries. It was democratic and strategic. It had pure lessons of politics and its machinations. It is obvious that stalwarts put their heads together, to produce a biological weapon of polls destruction, specifically modified for the 2023 polls of Naija. Will the APC do the same and even better? The who blinks first game has come to an end and PDP has blinked out its star -- a shooting star at that. There is no doubt whatsoever, about its star's brilliance and luminance. The APC needs a counter to that move. Someone with the prudence, the might, and the mind. Someone with antecedents as plain as day. A developer of capital, both human and financial. There is no reason why every state in the country cannot be a mini Lagos or even Lekki, and be self-subsistent. It will take time, a lot of innovation and resources. Above all, it needs a leader that can deliver. Infact, a leader that has delivered! 

 

Tahir is Talban Bauchi. 

 

Thursday, 19 May 2022

Mutane 29 Sun Mutu A Hadarin Mota A Kaduna, da Fashewar iskar gas a Kano Mutane 29 ne suka mutu a ranar Talata a wasu manyanalamura masu tashin hankali guda biyu a jihohin Kaduna da Kano. Lamarin na farko ya yi sanadin mutuwar fasinjoji 20 da suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da motar bas da suke ciki ta yi karo da tirelar siminti na BUA da misalin karfe 5 na safe. A Kano, an fitar da akalla gawarwaki tara daga karkashin baraguzan ginin da ya ruguje a unguwar Sabongari sakamakon fashewar iskar gas.Ginin yana dab da makarantar Winners Private School dake kan titin Aba. Wasu daliban makarantar sun samu raunuka a hatsarin. Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kaduna, Hafiz Muhammad, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin, ya ce sun yi zargin gajiyar da direban ne saboda sun fito daga tafiya dare. Ya ce, “Bas din ya yi karo da wata tirela ta siminti ta BUA sannan ta kama da wuta. Mutane 22 ne ke cikin motar bas din daga cikinsu manya maza 17, mata 2 da kuma karamar yarinya. “Sun ce tirelar tana fakin ne a lokacin da motar bas ta shiga karkashinta. Abun yayi muni. Kullum muna gargadin direbobin bas gamda tafiye-tafiyen dare,” inji shi. Ko da yake ya yarda cewa babu wata doka da ta hana tafiye-tafiye da daddare, shugaban hukumar FRSC ya ce, “Abin da ke tattare da hadari ne domin galibin hadurran da aka samu a wannan hanyar na faruwa ne saboda tafiye-tafiyen dare.” A Kano, an yi tashin hankali a Sabongari yayin da fashewar iskar gas ta girgiza yankin da kewaye har zuwa kafuwarsu. Sabongari yanki ne na mazauni da kasuwanci a karamar hukumar Fagge, wanda ya fi yawan jama’a da ba ‘yan asalin jihar ba. Wani dan agajin da ya taimaka wajen kwashe wadanda suka makale a ginin ya ce ya kirga gawarwaki tara amma ‘yan sanda da gwamnatin jihar sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai hudu da biyar. Akwai kuma wani sirri game da musabbabin fashewar.Yayin da ‘yan sanda suka dora alhakin fashewar wani bututun iskar gas a wani shagon walda da ke gaban makarantar, mazauna yankin sun ce harin kunar bakin wake ne. Wani mazaunin garin ya ce dan kunar bakin waken ya so shiga makarantar mai zaman kansa ne amma aka hana shi shiga sannan ya tarwatsa kansa, inda ya kashe wasu uku. Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Samaila Shu’aibu Dikko da Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a jihar Alhassan Mohammed, sun shaida wa Aminiya cewa rahoton farko ya nuna cewa fashewar ta fito ne daga shagon walda kuma ba ta kowace hanya fashewar bam bane. Gwamnatin jihar ta kuma tabbatar da wannan matsayin ta wata sanarwa da kwamishinan yada labarai,Muhammad Garba ya fitar, wanda ya bayyana mai walda Vincent Ezekwe daga jihar Enugu. Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya je Kano domin ganawa da wakilan jam’iyyar APC mai mulki a kan kudirinsa na shugaban kasa, tare da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci wurin da fashewar ta afku a jiya. Mataimakin shugaban kasan ,wanda wani mazaunin yankin da kwamishinan ‘yan sandan suka yi wa bayanin, ya ce “Mun zo nan ne domin mu gano abin da ya faru da kuma jajantawa mazauna yankin da iyalan da suka rasa ‘yan uwansu da wadanda suka jikkata. An bayyana mana cewa, fashewar wani abu ne daga shagon wani mai walda kuma da mai walda da wasu da dama, kusan tara sun rasa rayukansu sakamakon wannan lamari. Wannan abin bakin ciki ne kuma abin takaici ne matuka. Muna addu’ar Allah Ta’ala yajikan wadanda suka rasu.” Ganduje ya ce jihar za ta dauki matakin daidaita sana’ar walda a wuraren da jama’a ke da yawa domin kaucewa afkuwar lamarin nan gaba. Fasto Mike Ajibola wanda cocinsa ke da tazarar mitoci ya ce an ceto sama da dalibai 50 da wasu ‘yan tsiraru da suka samu raunuka. Daga: Firdausi Musa Dantsoho



 Mutane 29 ne suka mutu a ranar Talata a wasu manyanalamura masu tashin hankali guda biyu a jihohin Kaduna da Kano.

Lamarin na farko ya yi sanadin mutuwar fasinjoji 20 da suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da motar bas da suke ciki ta yi karo da tirelar siminti na BUA da misalin karfe 5 na safe.

A Kano, an fitar da akalla gawarwaki tara daga karkashin baraguzan ginin da ya ruguje a unguwar Sabongari sakamakon fashewar iskar gas.Ginin yana dab da makarantar Winners Private School dake kan titin Aba. Wasu daliban makarantar sun samu raunuka a hatsarin.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kaduna, Hafiz Muhammad, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin, ya ce sun yi zargin gajiyar da direban ne saboda sun fito daga tafiya dare.

Ya ce, “Bas din ya yi karo da wata tirela ta siminti ta BUA sannan ta kama da wuta. Mutane 22 ne ke cikin motar bas din daga cikinsu manya maza 17, mata 2 da kuma karamar yarinya.

“Sun ce tirelar tana fakin ne a lokacin da motar bas ta shiga karkashinta. Abun yayi muni. Kullum muna gargadin direbobin bas gamda tafiye-tafiyen dare,” inji shi.

Ko da yake ya yarda cewa babu wata doka da ta hana tafiye-tafiye da daddare, shugaban hukumar FRSC ya ce, “Abin da ke tattare da hadari ne domin galibin hadurran da aka samu a wannan hanyar na faruwa ne saboda tafiye-tafiyen dare.”

A Kano, an yi tashin hankali a Sabongari yayin da fashewar iskar gas ta girgiza yankin da kewaye har zuwa kafuwarsu.

Sabongari yanki ne na mazauni da kasuwanci a karamar hukumar Fagge, wanda ya fi yawan jama’a da ba ‘yan asalin jihar ba.

Wani dan agajin da ya taimaka wajen kwashe wadanda suka makale a ginin ya ce ya kirga gawarwaki tara amma ‘yan sanda da gwamnatin jihar sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai hudu da biyar.

Akwai kuma wani sirri game da musabbabin fashewar.Yayin da ‘yan sanda suka dora alhakin fashewar wani bututun iskar gas a wani shagon walda da ke gaban makarantar, mazauna yankin sun ce harin kunar bakin wake ne.

Wani mazaunin garin ya ce dan kunar bakin waken ya

so shiga makarantar mai zaman kansa ne amma aka hana shi shiga sannan ya tarwatsa kansa, inda ya kashe wasu uku.

Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Samaila Shu’aibu Dikko da Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a jihar Alhassan Mohammed, sun shaida wa Aminiya cewa rahoton farko ya nuna cewa fashewar ta fito ne daga shagon walda kuma ba ta kowace hanya fashewar bam bane.

Gwamnatin jihar ta kuma tabbatar da wannan matsayin ta wata sanarwa da kwamishinan yada labarai,Muhammad Garba ya fitar, wanda ya bayyana mai walda Vincent Ezekwe daga jihar Enugu.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya je Kano domin ganawa da wakilan jam’iyyar APC mai mulki a kan kudirinsa na shugaban kasa, tare da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci wurin da fashewar ta afku a jiya.

Mataimakin shugaban kasan ,wanda wani mazaunin yankin da kwamishinan ‘yan sandan suka yi wa bayanin, ya ce “Mun zo nan ne domin mu gano abin da ya faru da kuma jajantawa mazauna yankin da iyalan da suka rasa ‘yan uwansu da wadanda suka jikkata. An bayyana mana cewa, fashewar wani abu ne daga shagon wani mai walda kuma da mai walda da wasu da dama, kusan tara sun rasa rayukansu sakamakon wannan lamari. Wannan abin bakin ciki ne kuma abin takaici ne matuka. Muna addu’ar Allah Ta’ala yajikan wadanda suka rasu.”

 

Ganduje ya ce jihar za ta dauki matakin daidaita sana’ar walda a wuraren da jama’a ke da yawa domin kaucewa afkuwar lamarin nan

gaba.

Fasto Mike Ajibola wanda cocinsa ke da tazarar mitoci ya ce an ceto sama da dalibai 50 da wasu ‘yan tsiraru da suka samu raunuka.

Daga:  Firdausi Musa Dantsoho

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Jaruman Kannywood mata Da Suka janyo cece ku ce a shafukan Sada zumunta







 A yayin da jaruman Kannywood ke ci gaba da fuskantar kalubalen sana’a da zamantakewar al’umma a muhallinsu, wasu ‘yan wasan kwaikwayo mata sun tsunduma cikin  cece-kuce a tsawon shekaru nan.

 

Daga cikin irin wadannan al’amura na baya-bayan nan har da cece-kucen da ya biyo bayan wata magana da fitacciyar jaruma Nafisa Abdullahi ta yi game da iyaye su daina haihuwan yayan da bazasu iya kula dasu ba. Baya ga Nafisat Abdullahi , Akwai wasu ’yan fim guda hudu na Kannywood da suka janyo cece kuce a shafukan yanar gizo .

 Nafisat Abdullahi 

A ranar 16 ga Afrilu, Nafisat ta wallafa a shafinta na Tuwita, "Ku daina haihuwa yayam da baza ku iya kula da su ba. 

Wallafar Tweeta din ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, daga wasu 'yan arewacin Najeriya da suka fassara shi da cewa kira ne da ya sabawa tsarin ilimin Alkur'ani da aka fi sani da "Almajiranci", yayin da wasu ke ganin ba ta da 'yancin da za ta magance matsalar zamantakewar al'umma. kasancewarta yar wasan kwaikwayo.

Nafisa ta dage cewa matsalar ba ta shafi ta ko wasu masu gata ba amma ga yara masu tasowa da iyayensu ke turasu zuwa tituna da sunan karatun Alkur’ani.

 

Rahma Sadau

 

Za’a iya kwatanta Rahama Sadau a matsayin jarumar da ta fi kowa janyo cece-ku-ce, a Kannywood wadda ta ke tattare da labaran cece kuce biyo bayan sana’arta a matsayin jaruma.

A shekarar 2016, an dakatar da ita daga yin wasan kwaikwayo a Kannywood saboda fitowar ta a wani faifan bidiyo na waka inda aka gan ta tana rungume da mawakin Najeriya, Classiq. Daga karshe dai an yafe mata sannan ta koma wasan kwaikwayo.

Jarumar ‘yar asalin jihar Kaduna da ke fitowa a fina-finan Kannywood da na Nollywood, ta kuma haifar da zazzafar cece-kuce a shafukan sada zumunta kan wasu hotuna da ta wallafa a shafukanta na Instagram da Twitter a shekarar 2020. Hotunan dai sun janyo cece kuce Inda har ya janyo batanci Ga manzon Allah hakan ya kasance cin mutunci ga musulman arewacin Najeriya. al'amarin da ya sa daga baya ta nemi gafara ta cire hotunan.


Sadiya Haruna

 

Sadiya Haruna wata jarumar fina-finan Kannywood ce da ta yi ta janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta kan yadda ta wallafa hotunanta da bidiyon tsiraicin da yawancin masoyanta ke ganin ba su dace ba.

A watan Fabrairu ne wata kotun majistare ta Kano ta yanke wa jarumar hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida ba tare da zabin tara ba saboda bata sunan wani abokin aikinsu, jarumi Isa A. Isa.

 Ana tuhumar jarumar da bata sunan Isa a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta.

Fati slow

 

Jarumar Kannywood, Fati Usman, wacce aka fi sani da Fati Slow a kwanakin baya ta kasance abin ban dariya da cece-kuce a shafukan sada zumunta tsakanin 'yan arewacin Najeriya.

A cikin watan Fabrairu ne ta shiga takaddama da fitaccen mawakin Hausa, Naziru Sarkin Waka, kan wani faifan bidiyo na TikTok da ta yi tana kiransa da mazinaci (a matsayin martani ga ikirari da mawakin ya yi na cewa wasu ’yan fim na neman yin lalata da ’yan fim mata kafin a raba musu matsayi a fim). Daga baya da ya bata kyautan naira miliyan 1 ta ce ta yi nadamar wannan zargi kuma ta nemi gafararsa.


Hadiza Gabon

 

Anyi cece kuce a shafukan sada zumunta yayin da a shekarar 2019 aka ga fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Gabon, tana cin zarafin wata jaruma Amina Amal a wani hoton bidiyo na Instagram.

Gabon dai ta yi ikirarin cewa Amal na zarginta da kasancewa 'yar madigo wanda hakan ya sa ta fusata ta dauki wani faifan bidiyo tana dukan Amal, lamarin da ya tilasta mata ta amsa zargin karya ne.

Bidiyon ya harzukar da mutani dama daga cikin mabiyan jaruman biyu, lamarin da ya sa wasu kungiyoyi suka yi barazanar kai karar Gabon saboda cin zarafi. An dai ce wasu masu ruwa da tsaki a harkar masana’antar ne suka sasanta ‘yan fim din biyu

 

Daga: Firdausi Musa Dabtsoho