Yoghurt sanannen abinci ne kuma mai gina jiki, wanda ba kawai yana da
sauƙi ba ne kuma ya dace a ci yana da daɗi sosai.
Yin yoghurt a gida yana da sauƙi, baya buƙatar amfani da abun hadda
Yogurt, Crock-pot, ko Instant Pot.
Iya abin da kuke buƙata shine sinadarai guda biyu: cikakkiyar
madara mai inganci da yoghurt ɗin da aka yi ko siya.
Yin yoghurt a gida zai ba da damar dangin ku duka su ji daɗin
fa'idodin kiwon lafiya da ɗanɗano mai ɗadi na yogurt.
Yin yoghurt yana da sauƙi kuma yana da saukin sha.
Yawancin yoghurt ya dogara ne akan kayan farawa watto starter, kayan
farawan shine yoghurt wanda aka riga aka hada (yawanci ana saya) shi wannan
starter in ana saka shi a cikin madara da aka tafasa a bar shi ya zama
yoghurt.
Don yin Yoghurt
daga farko, kuna buƙatar:
·
1-3 lita na madara
·
Jakar starter culture ko karamar cokali 2 na yogurt mara siga
·
Ya kamata adadin madarar da aka ƙara ya kasance ƙarƙashin adadin
yoghurt da za ku samu a ƙarshe.
Yadda ake
hadda yoghurt
1. Da fari dai, sai
kizuba madararki a cikin babban tukunya a barshi har sai ya fara tafasa a ci
gaba da motsa shi don kada ya kone.
2. Na biyu, a
sauke madara daga wuta a ba shi damar yin sanyi zuwa kusan 40 ° C. Yi
amfani da ma'aunin zafi sai ku sanya hannun ku ciki domin tabbatar da
cewa yana da dumi kuma ba shi da zafi sosai da zai kone ki.
3. Na uku, saka
yoghurt Mara siga a cikin madaran mai dumi kuma a gayyata kayan haɗin har
sai sun hade a cikin madarar.
4. Na hudu, dafa
kwantena na yogurt inki da ruwan zãfi kafin a zuba duka yogurt in da aka
cakuda da madara a cikin kwantena.
5. Bayan haka, sai asa
kwantenan a cikin wuri mai dumi ko a rufe shi da barguna don kasancewa cikin
zafin. A bar shi na aƙalla awanni 8 sannan, a duba yogurt ɗin don
tabbatar da ya yi kauri.
6. Daga karshe
ki bar yoghurt dinki ya zauna a cikin firij domin yayi kauri, daga nan zaku iya
zuba masa siga, zuma ko ki cin shi yadda yake.
Yoghurt na gida zai iya ɗaukar har zuwa kwanaki uku a cikin firiji
ba tare da ya lallace ba.
By: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment