Gyambon
ciki shine buɗaɗɗen raunuka waɗanda ke tasowa akan rufin ciki. Hakanan
ana iya kiransu da gastric ulcer ko peptic ulcer a turance. Wannan Cutar na iya
shafar mutane tun suna ƙanana, amma sun fi yawa a cikin mutane sama da shekaru
60. Maza kuma sun fi samun matsalar gyambon ciki.
Ulcers na
faruwa ne lokacin da acid daga abinci mai narkewa ya lalata bangon ciki.
Mafi yawan abin da ke haifar da gyambon ciki shine kamuwa da cuta daga kwayoyin
cuta mai suna HELICOBACTER PYLORI. Na dogon lokaci mutane sun yi imanin
cewa gyambon ciki na faruwa ne ta hanyar wasu zaɓin salon rayuwa. Mutane
da yawa sun yi tunanin cewa cin abinci mai yaji da fuskantar damuwa suna da
alaƙa da ulcer, amma babu wata kwakkwarar hujja da ta tabbatar da waɗannan
abubuwan.
Gyambon
ciki na iya buƙatar salon rayuwa da canje-canjen abinci don sarrafa su yayin da
suke warkewa. Magungunan rage acid na iya zama da amfani. Kamar
yadda Akwai abinci da ya kamata mai gyambon ciki ya kaurace wa haka zalika
Akwai Mafi kyawun abincin da ya kamata ku ci idan kuma da gyambon ciki sun
haɗa da:
Abincin Mai dauke da Fiber
Wannan
ya hada da Alkama, hatsi, tsaba, gyada, lemu, tufa da karas.
Wadannan abinci suna da amfani a gare ku saboda suna iya taimakawa wajen hana
gyambon ciki tasowa.
Abincin Mai dauke da bitamin A
Abinci
kamar dankali Hausa, ganyen Kale, alayyahu na dauke da Vitamin A. Wadannan
abinci na kara samar da gamsai a cikin hanjin, wanda wasu ke ganin zai iya
taimakawa wajen hana gyambon ciki.
Koren shayi
Binciken
da ya fito ya nuna cewa koren shayi na iya taimakawa wajen yakar helikobacter
pylori.wadda hakan ke nufin yana da kyau masu gyambon ciki su yawaita
sha.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment