Doya da kwai wadda ake Kira da Yamarita da turanci abinci ne da
kowa Ke so a Najeriya, sai dai inhar ba'a gwada ba. Yamarita dafaffen
doya ne da aka sa a cikin danyan kwai, flawa, citta, tafarnuwa, da gishiri, sai
a soya. Wannan shi ne daya daga cikin shahararrun abincin Hausawa.
ya kuma shahara kamar yadda suya watto balangu ya shahara.
Yamarita yana da saukin hadawa kuma yana da dadi. Kuna iya
hada shi a cikin kusan mintuna 45 kawai. Ana iya hada yamarita
da stew, miyan kwai, ko ketchup .
Abubuwan da ake
bukata sune:
·
Doya- 1 kg
·
Kwai 3
·
Cokali 2 na flawa.
·
Man gyada (300ml).
·
Karamin Cokali na ginger.
·
Karamin Cokali na tafarnuwa.
·
1 teaspoon na barkono.
·
1 cube na knorr (mai zaki).
·
gishiri kadan
Wadannan sune Abubuwan da ake amfani da su wajen yin yamarita.
Yadda ake hada
yamarita
1. Da farko za'a fere bayan doyan, sai a yanka zuwa girma da sifan da
ake so sai a dafa na kamar minti 15. Har sai Yayyi laushi kuma ya dahu
sosai. Sai a juye a matsama a barshi Yayyi sanyi.
2. Sai a hada kayan kamshi duka ginger, tafarnuwa, barkono, Maggi,
gishiri da kwai ukun da aka fasa. Sai a jujjuya yadda ya kamata.
3. sannan sa a zuba doyan da aka dafa a ciki.
4. Sai a daura kwanon suya akan wuta sai a zuba man gyada a
ciki. Sai a barshi Yayyi zafi na kamar minti 1.
5. A zuba dafaffen doyan a cikin hadin kwai ɗin sai a zuba a
cikin mai mai zafi kuma a soya.
6. Idan ba Soyu sai a juya dayan bangaren, kar a bari ya
ƙone.
7. Idan ya soyu sai a kwashe aci tare da miyan da
mutum ya fi so ko Gasashen kifi ko kaji.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment