Yawanci, ana amfani da kanwa don haɗa shi, amma za ku iya maye
gurbinsa da abun da aka fi sani da ncha ko ngo wanda ya fi kyau
ga lafiya, ba ya kumbura ciki kuma ba zai sa ku yi zawo ba.
Abubuwan bukata
sune:
*Kafar saniya
*Man ja
* Kanwa
*NikakkenKa kwallon ehuru
*Crayfish nikakke
* Barkono nikakke
* Attarugu
* Albasa
* Kayan dandano
* Gishiri
* Ganyen Utazi
Yadda Ake hadda
Nkwobi Kafar saniya
1. Da farko zaki yanka ƙafar saniya zuwa girman da kike so, sai ki wanke,
ki sa a cikin tukunya.
2. Sai ki sa sinadaran dandanon ki, kayan kamshi, yankakken albasa da
ruwa kadan sai ki rage wutan zuwa matsakaicin zafi har sai ya dahu sosai. Sai
ki sa gishiri, ki motsa kuma ki tabbatar da cewa babu wani sauran ruwa a ciki.
3. A cikin wani kwano, sai ki hada kanwan ki da ruwa kadan sai ki motsa.
Sai ki tace hadin da kyau a cikin wanni kwano mai kyau sannan ki ajiye a
gefe.
4. Ki zuba man jan ki daidai a cikin busasshiyar tukunyar ki da
aka bushar sannan a zuba hadin da aka tace a ciki kadan_kadan, ana rika motsawa
da muciya har sai man jan ya koma rawaya kuma ya yi kauri.
5. Sai ki sa crayfish nikakke, barkono da ehuru. Sai a juya sosai
har sai komai ya haɗu yada ya kamata
6. Sai a zuba ƙafar saniya da aka dafa a cikin man jan kuma a
motsa sosai tare da muciya.
7. Sai a mayar kan murhu a dumama.
8. Toh Nkwobi ya hadu sai a shirya nkwobi a kwano A yi masa ado da
zoben albasa da yankakken ganyen utazi.
By: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment