Kuna da bukukuwa da kuke ɗaukin yi? Kuna da wani biki da kuka rasa
wanni irin miya zaku dafa? Idan eh, ya kamata ku gwada Miyan Taushe kuma
za ku yi farin ciki da yin hakan. Miyan Taushe abinci ne na Arewacin Kasar
Najeriya kuma Hausawa da Fulani ne ke cin sa. Miya ce da ake hadda wa da
kabewa (pumpkin) kuma galibi ana cin sa lokutan bukukuwa, amma wasu suna
ɗaukar sa a matsayin abinci na asali (kamar don abincin rana ko abincin dare).
A cikin wannan girke-girken namu na yau, zan koya muku yadda ake hadda Miyan
Taushe.
Miyan Taushe yana da sauƙin dafa wa, ga daɗi sosai, kuma yana da
sinadarai masu gina jiki. Ku bi ni yayin da nake ɗaukar ku ta hanyar
matakan yadda ake hadda shi.
Abubuwan bukata don
hada Miyan Taushe
Kuna buƙatar abubuwan da ke gaba don yin Miyan Taushe:
*kabewa (pumpkin) guda daya
* kofi daya na man ja ko man gyada
*½ kofin gyada (nikkaken gyada)
*Nikkaken tumatir
*Nikkaken Barkono
*Alayyahu yankakken
*Albasa niƙkake
*Kayan kamshi da dandano kamar thyme, curry, maggi, da gishiri.
*Kifi ko nama
*Kofuna 3 na ruwa
Yadda ake hadda
miyan taushen
1. A dora tukunya mai tsafta a wuta sannan a zuba man ja ko man gyada.
2. A Yanka albasa a saka a cikin tukunyan.
3. A bar albasan ta soyu na tsawon mintuna 3 zuwa 5 a ƙarƙashin matsakaicin zafi har sai ta zama launin ruwan kasa.
4. A zuba niƙkaken tumatir, barkono, da albasa. Sai a
soya na minti 10.
5. A yanka kabewan a zuba a tukunyar ya dafu.
6. A Ƙara kofuna 2 na ruwa a tukunyar dafa miyan kuma.
7. Sai a sa kifi ko nama a cikin tukunyar dafa miyan sai a bashi
damar dafuwa na mintina 20.
8. Sai ki Yanka ƙarin albasa ki ajiye su a gefe tare da yankakken
alayyahun ki.
9. Ki sa gyadan ki niƙkake a cikin tukunyar miyan ki sai a dafa na
mintuna 5 zuwa 8.
10. Sai a sa kayan ƙamshi da dandano(maggi, curry, gishiri, da dai
sauransu) sai a kuma motsa miyan da kyau. A Ba sa minti 10 ya dafu.
11. Ku ɗanɗana domin tabbatar da komai ya daidaita
idan akwai buƙatan kari sai a kara.
12. A Rage zafin wutan sai a zuba albasa da yankakken alayyahu a ba shi
damar ya turara na mintuna 10 zuwa 15.
13. Shi kenan Miyan Taushen ku ya haddu.
A gargajiyance, galibi ana cin Miyan Taushe da Tuwon Masara, Tuwon
Shinkafa, Tuwon Alkama, Tuwon Dawa, masa da sinasir.
By: Firdausi Musa
Dantsoho
No comments:
Post a Comment