Ministan
aikin noma da raya karkakara, watto Sabo Nanono ya auri yarinya mai shekaru 18 a ɗaurin auren da aka yi cikin sirri kamar yadda
muka samu rahoto daga Daily Nigerian. Nanono, mai shekaru 74 ya auri kyakkyawar
yarinyar a auren sirri da mutum uku daga danginsa kadai suka hallarci ɗaurin
auren da aka yi a Jere a jihar Kaduna. "Mutane uku kawai ministan ya
wakilta kuma ya gargaɗe su da kada su bayyana wa mutane cewa ya yi aure,"
a cewar wani majiya daga iyalin da ya nemi a boye sunansa. Haka zalika Daily
Nigerian ta gano cewa tuni amaryar ta tare a gidan Ministan da ke Tarmandu
Close a Kano. Duk da cewa iyalan ministan ba su yarda auri yarinyar da ya girma
da shekaru 50 ba, majiyoyi sun ce ya tsaya kan bakansa sai da aka yi auren.
"Ministan ya tsunduma kogin soyayya. Bisa dukkan alamu babu abin da zai
sauya masa ra'ayi," a cewar majiyar.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment