Kamar yadda Binciken kimiyya ya bayyana cewa, bayan karin dandano da karas yake karawa abinci yana kuma dauke da sinadarai masu yawa da suka hada da antioxidants, beta-carotene, alpha-carotene, lutein, potassium, vitamin C, vitamin A, fibre da Carotenoids.
Shi karas yanada kyau sosae domin
kuwa yana kara inganta lafiyar ido, yana Gyara fatan jiki, yana Taimakawa
wurin kiyaye kamuwa da ciwon daji (kansa) da sauransu.
A yau zamu koya maku yadda ake hada lemun karas
ABUBUWAN
DA AKE BUKATA SU NE:
Karas
Cittah
Sugar
Flavour
abarba
YANDA
AKE HADAWA
1.
Da farko zamu wanke karas dinmu , ya wanku sosai sai mu yanka kanana mu zuba a bilenda.
2.
Sai mu wanke cittan mu itama
a yanka kanana sai a zuba a
bilenda shima abarban a sa a bilenda a
sa ruwa a markada da karas din, yayi laushi.
3.
Sannan sai a tace a sa sugar da
flavour.
4.
A juya sosae sae ki sa a firinji
yayi sanyi a sha lafiya.
Rubutawa: Firdausi Musa
Dantsoho
No comments:
Post a Comment