Friday, 30 April 2021

YADDA AKE HADDA BATTERED PLANTAIN

 


Yanna da gundura ace a ko da yaushe idan mutum zai ci plantain sai dai ya soya ko kuma ya dafa, shiyasa yau zamu kawo maku watta sabuwar hanya da zaku bi domin jin daddin plantain inku a sauwake kuma ba sai kun kasha kudi ba.

Ana kiran wanan hadin battered plantain.



ABUBUWAN BUKATA SUNE:

·       Plantain

·       flawa

·       Kwai

·       Baking soda dan kadan

·       Sinadarin dandano

·       Yaji

·       Gishiri

·       Man gyada



YADDA AKE HADAWA

1.   A cikin kwanu mai tsafta mu fasa kwan mu a ciki, sai mu zuba sinadarin dandanon mu, yaji, gishiri, baking soda sai mu juya ya hadu.

2.   A cikin haddin kwan, mu zuba flawa da dan ruwa sai mu juya har sai komai ya hadu kuma hadin yayyi kauri.



3.  Sai mu bare plantain, mu yanyanka shi shape in da muke so.

4.  Sai mu tsoma plantain in mu cikin kwabin flawa, mu tabbatar flawan ya kama plantain in sosai.



5.   Daga nan sai mu sa plantain in mu da  muka rufe kwabin flawan cikin man gyada mai zafi mu soya .

6.   In plantain in yayyi brown sai mu kwashe.

7.  Toh battered plantain in mu ya haddu. Aci lafiya.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

 

 

Thursday, 29 April 2021

YADDA AKE HADA YOGHURT SALAD




Shi wannan salad in na daban ne ba irin waenda kuka saba gani bane, ana hadda wannan salad in ne da yoghurt da kuma iyayan itatuwa, kuma yana da saukin hadawa baya daukan fiye da minti goma sha biyar wajan hadda shi.

Wannan salad in yana da daddi kuma ya na da kosarwa.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

·         Yoghurt

·         Strawberries

·         Seedless Grapes

·         Ayaba

·         Tufa

·         kwakwa

·         Condensed milk

 

YADDA AKE HADAWA

1.       Zamu farad a wanke iyayan itatuwan mu tas.

2.       Sai mu yanyanka ayaba, tufa da strawberries inmu kanana.

3.       Shi graphes in tunda seedless ne zamu barsh a kwaya kwayansa, sai mu kankare kwakwa watto grating kenan.

4.       Zamu samu kwanu mu na salad watto salad bowl,mu zuba yankaken iyaya itacen mu a ciki.

5.       Sa’annan mu zuba yoghurt in mu a kai mu gauraya.

6.       Idan ya hade gabaki daya sai mu zuba condense milk mu juya.

7.       A sa a fridge yayyi sanyi sai a sha lafiya.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

YADDA AKE HADDA CHOCOLATE CUPCAKE

 


Chocolate cupcake, cake ne amma na chocolate kuma cake ne da ake yinsa a kananan kofin hada cake, yana da zaki ga daddi ga kuma saukin hadawa.



ABUBUWAN BUKATA SUNE:

·         Flawa kofi biyu

·         Siga kofi daya da rabi

·         Cocoa powder kwatan kofi

·         Kwai guda  biyu

·         Vanilla flavour cokali daya

·         Man gyada rabin kofi

·         Madara kofi daya

·         Nescafe dan kadan

·         Bakar hoda cokali daya

·         Baking soda cokali biyu

·         Ruwa kofi daya




YADDA AKE HADAWA

1.       Da farko zamu samu roban mu mai tsafta sai mu zuba flawan mu kofi biyu, siga kofi daya da rabi, bakar hoda cokali daya, baking soda cokali biyu, sai mu juya su gabaki daya.

2.       Daga nan sai mu zuba cocoa powder kwatan  kofi sai a kara juya wa, wannan hadin su ake kira dry ingredients.             


3.       A cikin wanni kwanu daban mu zuba madaran mu na ruwa kofi daya, man gyada rabin kofi, kwai guda biyu sai mu juya, wadannan sune wet ingredients.

4.       Sai mu dauko hadin madaran mu watto wet ingredients, mu zuba acikin hadin flawan mu watto dry ingredients sai mu juya domin komai ya hade da kyau.                     


5.       Idan komai ya hade zai mu zuba flavour in mu.

6.       A cikin tafashashen ruwan  kofi daya mu sa nescafe dan kadan, mu juye a cikin kwabin cake in mu .             


7.       Mu tabbatar muna juye tafasashen ruwan, mu juya shi agurguje domin kar yayyi gudaji.

8.       Sai mu samu tray in cup cake in mu, mu sa cupcake paper in mu, sai mu zuba rabin kofin kwabin cake in mu a cikin  kowanni cupcake papper .                                                          


9.       Sai mu sa, a oven mu gasa na minti ashirin, toh chocolate cupcake in mu ya hadu.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

 

 

Wednesday, 28 April 2021

YADDA AKE HADA GARIN KUNUN TSAMIYA DA KUNUN TSAMIYA



Yin garin kunun tsamiya wanni hanya ne da zaku bi domin rage wa kanku aiki, shi de kunun tsamiya kunu ne da yake da dadi ga saukin yi kuma ana amfani da tsamiya ne wajan hada shi.

Ayau a shafin mu na tozali zamu koya maku yadda ake hadda garin kunnun tsamiya das hi kunun tsamiyan.





ABUBUWAN BUKATA WAJAN HADDA GARIN SUNE:

·         Gero

·         Kanunfari

·         Masoro

·         Barkonu

·         Busasshen citta

 

YADDA AKE HADDA GARIN KUNUN TSAMIYAN

1.       Zamu farad a wanke geron mu tas, sai mu shanya shi ya bushe.

2.       Sai mu zuba su kayan kamshin mu su, kanumfari, citta, barkonu, masoro, mu kai nika .

3.       Mu tabbattar enjin babu ruwa kuma za,ayi mana nikan gari ne.

4.       Toh garin kunun tsamiyan mu ya haddu.

 


YADDA ZAMU HADDA KUNUN TSAMIYAN MU

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

·         Garin kunun tsamiya

·         Tsamiya

·         Siga ko zuma

 


1.       Zamu wanke tsamiyan mu, sai mu jika idan ya jiku sai mu tace a cikin tukunya mu kara ruwa mu barshi ya tafaso.

2.       Idan ya tafaso sai mu kwaba garin kunun tsamiyan mu da ruwa ya dan yi kauri ba sosai ba.

3.       Sai mu zuba  ruwan tsamiyan daya tafasa a cikin kwabin garin kunun tsamiyan .



4.       Idan kunun ki baiyi kauri ba zaki iya mai dashi kan wuta ki yi ta juyawa har sai yayyi kauri, da zaran kunun ki yayyi kauri to kunun tsamiyan ki ya hadu

5.       Sai a zuba siga ko zuma asha lafiya

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

TITTLE: MUHIMMANCI ALLURAN RIGAKAFI GA YARA KANANA

Alluran rigakafi sunada matukar muhimmanci ga rayuwar yara kanana domin kuwa a wannan lokacin basuda wata wadatar wani garkuwar jiki da zai kare su daga kamuwa da cututtuka musamman daga ranar haihuwa har zuwa shekara biyar a rayuwa. Alluran rigakafin yara sun kasu kashi iri-iri wadda a kowane wata ana yinsa kama daga ranar haihuwa har zuwa lokacin da yaro zai shekara hudu zuwa biyar a duniya, wadannan allurai sun hada da  BCG,BPT,HPV,CSM, YELLOW FEVER DA KUMA MEASLES.Da sauransu.

Wadannan allurai suna kare yara daga kamuwa da cututtuka masu saurin hallaka yara kamar su tarin fuka,tarin shika ciwon shawara, ciwon hanta da dai sauran cututtuka masu matukar hadari ga lafiyarmu, haka zalika wannan allura ta rigakafin yara ba duka ne ake allura ba akwai wadda ana disawa ne abaki kaman su cutar shan inna,polio,sankarau da sauransu.ana fara wannan allura ne Jim kadan bayan an haifi yaro an tsabtaceshi a asibiti kuma shiyasa ake so ana haihuwa a asibiti domin yanada matukar amfani da zaran an haifi yaro kan ya koma gida ake mishi alluran farko na tarin fuka wato BCG.

Don haka iyaye mu kula sosai domin yiwa yayanmu wannan alura don kare su daga shiga cututtuka masu hadari, haka zalika ita wannan allura ba wai a lokaci daya ake yinsu duka ba tsakanin na farko da na biyu yana iya kaiwa kwana 40 wato mako 4 zuwa 6 amma ya danganta da bayanin maaikatan kiwon lafiya.


Haka zalika duk yaran da iyayensu ke kaisu asibiti don karbar alluran rigakafi ana ganinsu cikin koshin lafiya da kumari, ga kuma kaifin basira da girma cikin sauri, don haka iyaye mu kiyaye sosai wajen kai yayanmu gurin rigakafi domin inganta lafiyarsu muma kuma zamu samu kwanciyan hankali wajen rage kashe kudi zuwa asibiti

BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR 



THE DIFFERENCE BETWEEN LOVE AND OBSSESSION

 

Many people can't differentiate between love and obsession as the magnitude of the feelings are almost the-same . To be fair, it's easy to confuse the two. Falling in love takes a lot of risk. In order to be in a truly emotionally fulfilling relationship, you need to be able to be vulnerable and allow another person in.

 For a lot of people, that can be pretty scary when you don't know how your partner feels. This state of the unknown can create a feeling of anxiety that won't really go away until you know for sure that your partner reciprocates your feelings. 

In a healthy relationship, both partners will be able to say how they're feeling and that anxiety would go away when that is established . But if that feeling of anxiety is still there, it can lead to obsession. So if your partner does any of these things,  it may not be love but obsession: 

1, 
Moving things too fast in the relationship  : 

 When someone is obsessed and not in love  the actions they take will most likely be driven by an anxiety that's caused by their obsession. "In obsession, we take that jumble of mixed or anticipatory anxiety emotions and shift it into our thinking…For instance, if someone has a fear of losing you, they're going to act in ways that ensure you're not going to leave them. That may include asking for exclusivity or commitment fairly early on in the relationship. More often than not, people are unaware it's happening. They're more likely to associate those anxious feelings of needing someone with love.

2, They do things in order to get your approval: 

Love is reciprocal. There should be a pretty equal amount of give or take. But when someone is obsessed, they're more likely to give more than they take . There motivations behind their giving will come from a place of wanting to please and be approved rather than love.

3, 

You Get the Feeling that they don't completely support you: 

When someone is obsessed with you, they might not like the idea of you growing as a person or having any independence. For instance, if you get a promotion at work, they may not seem as happy and excited for you because they're thinking about how your promotion might change your relationship. But in healthy love, each partner empowers one another to be the best version of themselves. Your partner will be excited for you and will support you as you grow as an individual.


BY STEPHANIE E. HEMEN

LOVE TRIANGLE AND HOW TO DEAL WITH IT

 


A love triangle also called a romantic love triangle or a romance relationship is usually a romantic relationship involving three or more people.


While it can refer to two people independently, romantically linked with a third, it usually implies that each of the three people has some kind of relationship with the other two. 

Although the romantic love triangle is formally identical to the friendship trade, as many have noted their actual implications are quite different. Romantic love as typically viewed as an exclusive relationship, whereas friendship is not. Statistics suggest that, in both western  and African society, willingly or not, most adults have been involved in a love triangle.

You might want to examine your place.

In the course of my research I discovered that there are two primary forms of love triangle, the rivalries and the split object.

In the rivalry, you are one of the two people competing for the exclusive love of the third person. In the split object, you are the person whose affection is divided between two lovers.

 Split objects relationships can also be imaginary. This occurs when someone imagines that they are in love with a romantic partner they have never met, or idealizes a relationship from their past.

  You may not have initially chosen your role in the rivalries love triangle. You may instead consider yourself a victim of another person’s adultery. While this may be initially true, if you’ve decided to try to stay within the relationship you are actively choosing a role. It may help you to be honest about this.

Discussing what happened, while talking about or hearing about a love triangle is difficult, it is important to be open and honest. Do all three people know about the triangle­­­…while being honest about a love triangle may be difficult, it is ultimately recommended by most experts. Lack of honesty within a relationship can be corrosive and damaging to everyone in the triangle, including yourself.


BY STEPHANIE E. HEMEN






KUNUN MADARA (MILK PAP OR MILK PUDDING)

 


Kunun madara, kunu ne da keda daddi sha, ga kuma saukin yi, baya bukatan kashe kudade da yawa wajan hada shi, kuma madara shine abu mafi muhimmanci wajan hada shi.

 


ABUBUWAN BUKATA WAJAN HADA SHI SUNE:

·         Madaran gari kofi biyu

·         Siga yadda kake son yayyi zaki

·         Kuskus kofi daya

·         Kanunfari kwaya shida

·         Corn flour four babban cokali daya

·         Vanilla flavor

·         Dan kishiri kadan

 

 


YADDA AKE HADAWA

1.       Da farko zamu zuba ruwa kofi hudu a tukunya.

2.       Sai mu sa madaran mu kofi biyu a cikin ruwan mu gauraya ya hadu mu tabbatar babu guda gudan madaran.



3.       Sai mu zuba gishiri kadan da kanunfarin mu, mu rufe tukunyanmu a barshi ya tafasu.

4.       Bayan ya tafaso zamu ji madaran mu na kamshi, sai mu saka kuskus in mu muyi ta gauraywa har sai kuskus in mu ya dahu.



5.       Idan kuskus in mu ya dahu, mu zuba sikarin mu, sai mu dama corn flour in mu da ruwa yayyi kauri sai mu zuba a cikin ruwan madaran.

6.       Toh kunun madaran mu ya hadu asha lafiya.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

Jaruma Rukayya Dawayya Ta Gina Katafaren Gida

 


Fittacciyar jaruma kuma mai shirya fina_finai a Kannywood rukkaiya umar santa wadda akafi sanni da rukkaiyya dawayya ta gina katafaren gida.

Kamar yadda jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, jarumar ta sanya hoton ta wadda a bayan ta zaga hangi katafaren gida wadda aka kusa kamalawa ta kuma yi rubutu kamar haka “ Masha Allah lah kuwwata illah billa”

Wanda jarumai yan uwanta maza da mata dama mabiyanta da masoyanta suka taya ta murna kera wannan Katafaren gida wanda itama yanzu tabi sahun jarumai masu manyan gidaje.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

Tuesday, 27 April 2021

LEMUN TSAMIYA



Tsamiya na daya daga cikin 'ya'yan itatuwa da Al'ummar Hausawa ke amfani dasu sosai a rayuwar su ta yau da kullum.Tana da amfani mai tarin yawa. Ana  sarrafa tsamiya a matsayin kayan sha, inda a yau wajaje dadama wasu kan qullata a leda ko gora bayan sun taceta sun gaurayata da sukari sai su sakata a na'urar sanyi(refrigegrator) wadda ayau haka zamu koya maku.





Wasu kuma sun dauketa a matsayin magani da kuma sarrafata a matasyin abinci domin akan yi kunun tsamiya da kuma tuwon tsamiya a wasu yankunan arewacin nijeriya.

 

ABUBUWAN BUKATA: 

*Tsamiya

*Citta

*Kaninfari

*Mazarkwaila ko siga

*Abarba



 YADDA AKE HADAWA

  1. Da farko Ki jika tsamiyarki idan ya jiku sai ki juye a tukunya ki xuba citta d kaninfari ki tafasa sai ko tace idan ya huce.
  2. saiki markade abarban ki ki tace ki zuba a cikin lemun tsamiya

 


      3. Daga nan saiKi saka mazarkwaila ko siga ki gauraya sai ki saka a fridge yayyi sanyi asha lafiya.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho