Plantain ba su da
tsawon rai. Kafin ku yi kefta idonku sau biyu, ya rube.
Ana ganin plantain a
matsayin abin maiƙima ga mutane kaɗan kawai saboda tsadar su. Don haka, lokacin
da kuka siye su a ƙarshe, baza ku so ya ɓace ba.
Don haka, menene
hanyoyin sarrafa da kuma adana plantain
1. Soyayyen plantain
Wannan shine abin da
yawancin mutane suke amfani da plantain suyi. Yawancin mutane suna son soyayyen
plantain, wanda aka fi sani da dodo.
Dabara anan ita ce
siyan plantain waɗanda bai gama nuna ba, ta wannan hanyar yana iya dadewa ba
tare da ya ɓace ba. sai dai, kuna son soya shi gaba ɗaya.
2. Plantain da wake
Hanya mafi sauƙi don
jin daɗi plantain da kuke ɗashi shine haɗa shi da wake. Plantain da wake abinci
ne mai daɗi.
3. Gasashen plantain
Wannan shine abin da
galibi ake kira 'Bole'. Kuna iya yin Bole a gida idan kuna da abin gashi. Ku ci
da gyada ko gasasshen kifi don more rayuwan ku.
4. Dafaffen plantain
Ga waɗanda ke guje wa
cholesterol da ke da alaƙa da soyayyen abinci, dafaffen plantain ko da yaushe
zaɓi ne mafi kyau. Bugu da ƙari, lokacin da kuka lura cewa plantain ɗinku suna
yin taushi koyaushe kuna iya dafa shi.
5. Faten plantain
Tabbas, zaku iya
sarrafa plantain kuyi fate da shi. Kar a manta idan ana hadda faten a
ƙara masa ganye da kayan lambu don kara masa daddi.
By: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment