Ruwa abin sha ne mai cike da abubuwan ban mamaki wanda ke kashe mana kishi da kuma taimaka muna wajan warkewa daga cututtuka daban -daban. Ruwa yana
da Amfani wajan warkar da cututtuka iri -iri waɗanda za su iya afkawa manya da
ƙanana. Shan isashen ruwa zai taimaka
wajan fitar da guba, zai kuma rage yawan kamuwa da cuta. Ko ta wace
hanya, yana da mahimmanci a sha ruwan mai kyau don gujewa kamuwa da cutar
da ruwa mara kyau ke ɗauke da
Na daya Ciwon koda
Ciwon koda na iya haifar da abubuwa iri -iri, ciki har da cutar
mafitsara ko na mara. Idan kuna da cystitis wadda E. coli ke jawowa,
yakamata ku sha ruwa da yawa. Ana wanke kwayoyin cutar microscopic na mafitsara
ta hanyan shan ruwa, wanda ke taimakawa wajen yaƙar kamuwa da cutar.
Yawan shan ruwa sau da yawa yana hana taruwar gishiri ko wasu dati ginuwa
a cikin fitsara, wanda ke sa masa kasala. Hydration wata hanya ce mai kyau
wajan tsabtace kodan da murmurewa daga cututtukan koda a mafi yawan lokuta.
Koyaya, ruwan da kuke sha bai kamata ya kasance gurɓatace ba, saboda yana iya
jawo wasu matsala.
Na biyu Ciwon fungal
Daya daga cikin hanya mafi inganci don yaƙar cututtukan yisti shine
amfani da ruwa. Duk da cewa akwai hanyoyi da yawa don magance cututtukan yisti,
amma magani mafi inganci shine ruwa. Yisti yana haifar da kamuwa da cuta
ta hanyar cin sukari a jikin ku. Lokacin da kuke shan isasshen ruwa, ana tace
sukari daga jikin ku, wanda ke rage haɗarin kamuwa da cutar yisti a jikin
ku. Don hana kamuwa da cututtukan fungal, yana da mahimmanci a sha ruwa mai
tsabta, mara guba.
Na uku Cutar numfashi
Da yawa daga cikin mu ba za su san yadda ruwa yake da tasiri wajen
magance asma da sauran cututtukan numfashi ba. Cututtukan ƙwayoyin cuta na fili
na numfashi sun zama ruwan dare, musamman idan yanayi ya canza. Mutumin da ke
fama da cutar numfashi na iya samun alamu kamar saurin numfashi, belching, da
motsin hanji, duk rashin ruwa a jikinsu ke haifar da Duk waɗannan
matsalolin . A irin wannan yanayi, shan ruwa yana da mahimmanci, kamar yadda
cututtukan numfashi ke haifar da rashin ruwa.
Na hudu Hawan jini
Ruwa yana taka muhimmiyar rawa wajen magance hawan jini. Ruwa yana
taimakawa wajan kara yawan jini a jikin mutum, yana sauƙaƙa wa zuciya
shigar da jinin cikinta. Rashin ruwa yana haifar da acidification na
jini, wanda ke haɓaka matakan LDL cholesterol. shan ruwa yana tsaftace
jinin ku kuma yana share cholesterol mai yawa wanda ya taru a cikin jikin
mutum.
Na biyar Ciwon kai na migriane
Mutanen da ke fama da Ciwon kai na migraines na iya samun fa'idodi
da yawa daga shan ruwan. Babban dalilin migraines shine rashin ruwa,
wanda shine dalilin da yasa kuna buƙatar kasancewa cikin ruwa a ko da yaushe.
Yakamata masu fama da ciwon kai su kula da shan ruwa da tabbatar da
isasshen ruwan sha a jikin su.
By Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment