Monday 4 July 2022

Fasto a jihar OndoYa Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yayi garkuwa da Mutane Sama Da 70

 


 Naija News ta rahoto a baya cewa jami’an tsaro a ranar Juma’a da daddare sun kubutar da wasu yara da dama da ake zargin an yi garkuwa da su tare da ajiye su a wani rukunin coci a unguwar Valentino a cikin garin Ondo, hedikwatar karamar hukumar Ondo ta Yamma a jihar Ondo.

 

Bayanan da ‘yan jarida suka samu tun da farko sun ce yaran wadanda yawansu ya haura 40, an kulle su ne a wani dakin da ke karkashin kasa a cocin bayan an yi zargin an yi garkuwa da su.

A cikin wani faifan bidiyo, an ce jami’an tsaro ne suka kai yaran da aka ce ba za su iya tunawa da sunayensu ba zuwa ofishin ‘yan sanda a cikin wata motar sintiri.

 

"Akwai yaran da aka yi garkuwa da su a cikin dakin da ke karkashin kasa na coci a yankin Valentino na Ondo," an ji wata murya tana cewa a daya daga cikin faifan bidiyo na yanar gizo.

 

Rahotannin da ke fitowa daga baya sun nuna cewa wadanda aka yi garkuwa da su 77 ne. Wadanda abin ya shafa sun hada da yara 25 da kuma manya 52, wanda adadinsu ya kai 77.

Da yake magana a hedkwatar ‘yan sanda da ke Igbatoro Akure, limamin da aka kama, Anifowose, ya ce ya samu umarni daga Allah cewa ya yi sansani har zuwa zuwan yesu na biyu.

 

“Ni ne na karɓi umarni daga Allah cewa mutane su zauna a coci kuma su jira zuwansa na biyu. Kuma membobina suna jiran zuwan Yesu na biyu lokacin da ’yan sandan suka mamaye cocin suka kama mu,” in ji Anifowose.

 

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho

 

No comments:

Post a Comment