Malaman
Jami’o’i (ASUU) ta ce yajin aikin da suke yi zai kare nan take idan
gwamnatin tarayya ta magance matsalolin su.
Shugaban
ASUU, Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake magana a gidan
talabijin na Channels TV’s Politics today a daren Litinin.
Osodeke
ya yi ikirarin cewa an cimma yarjejeniya da gwamnati, amma ba a sanya hannu ba.
A
cewarsa, dagewar ASUU na yin amfani da nasu tsarin biyan kudi, university
Transparency Accountability Solution (UTAS), babbar bukata ce.
“Game
da maganar ASUU, ana iya kawo karshen yajin aikin gobe.
“Mun
kammala tattaunawar. Idan gwamnati ta kira mu yanzu mu zo mu rattaba
hannu kan yarjejeniyar, gobe za mu kasance a can.
“Gwamnati
ta gaya mana sun gama gwajin UTAS kuma mun amince da shi, sannan za mu
janye yajin aikin.
“Yaushe
za su sanya hannu kan yarjejeniyar? Yaushe zasu karbi UTAS?
Wadannan su ne tambayoyi biyu da ya kamata mu yiwa gwamnatin Najeriya,” in ji
Osodeke.
No comments:
Post a Comment