Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya lashe zaben fidda gwanin
takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka kammala a ranar Asabar da ta
gabata.
Atiku ya lashe zaben ne da kuri’u 371 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, wanda ya samu kuri’u 237 bayan Tambuwal ya janye wa Atiku.
Kakakin tambuwal ya ce Tambuwal ya sauka ne sakamakon kishin kasa da
yake nuna wa ci gaban Najeriya.
Bayan zaben fidda gwani na shugaban kasar a jam'iyyar APC wadda
Atiku ya lashe Yanzu kallo ya koma ga jam'iyyar APC inda mutane ke ta tofa
albarkacin bakinsu game da shin wa zai lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar.
Haka zalika mutani na ganin cewa idan jam'iyyar APC bata zabi wadda ya dace ba Jam'iyyar PDP na iya kada ita a babban zabe sai de kuma a ranar talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnoni da kuma shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu a fadar shugaban Kasa kafin ya tashi zuwa taro a kasar Spain.
A taron, Buhari ya gargaɗi gwamnoni da shugaban jam’iyyar da su tabbata an samu haɗin kai a cikin jam’iyyar domin a zaɓi ɗan takara mai nagarta da kishin talakawa wanda ko bayan ya ci zaɓe zai yi tasiri a zukatan ƴan ƙasa.
Bayan haka shugaba Buhari ya ce shi da kansa ya ke so ya zaɓi wanda zai gaje shi, Kuma abinda kawai yake buƙata shine goyon bayan gwamnoni.”
Ya bayyana cewa yana shekarasa ta karshe a zangon mulkisa ta biyu, dole
ne ya maida hankali da jajircewa wajen tsayawa tsayin daka domin ganin
Jam’iyyar APC bata kauce hanya ba.
Yace Akidun da suka kakkafa da suka rike jam’iyyar ba za su bari su ruguje ba. Saboda haka dole su hakura da juna su yi abinda ya dace.
A karshe shugaba Buhari ya ce abinda jam’iyyar ya kamata ta maida
hankali akai yanzu shine su ga sun yi nasara, kuma hakan na bukatar dole kowa
ya ajiye burin sa ya zo gabaɗaya a yi abinda ya dace domin cigaban jam’iyyar
APC.
Hakan na nufin , "Jam'iyyar APC ba zatai zaben fidda gwani ba, za'a fitar da dan takara ne ta hanyar masalaha kamar yadda akai a lokacin samar da sabon shugaban Jam'iyyar a matakin kasa".
Jagoran jam'iyyar APC na kasa Bola Ahmad Tinubu, ya ce ba wanda zai
janyewa cikar burinsa na zama Shugaban kasa, ya kuma yi gargadin cewar matukar
ba'a zabe shi a dan takara ba gwara kowa ya rasa.
A zaman da shugaban kasa ya jagoranta da gwamnonin APC kafin ya tafi kasar Spain, an ruwaito cewar, An watse baranbaran tsakanin gwamnonin jam'iyyar APC kan wanda zai yi takarar shugaban kasa a 2023, inda gwamnonin Arewa suka ce dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu ba zai iya kada Atiku Abubakar ba, a don haka dole sai dai a bawa dan ƴankin Arewa takara.
A hannu guda kuma suma gwamnonin yankin Kudu sun ce ba su yarda ba.
Akwai kuma raɗe-raɗin cewa kusan dukkanin ƴan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin Jam'iyyar APC zasu janyewa Furofesa Yemi Osibanjo kafin ranar zaɓen fidda gwani ko kuma a ranar.
Idan ta tabbata to Osibanjo zai fafata da Alhaji Atiku Abubakar da kuma
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
By: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment