Idanun da
suka rikide suna daya daga cikin matsalolin idanu da jarirai suka saba
fuskanta. Wannan cuta wacce kuma aka fi sani da strabismus yana
tafiya da kanshi, amma a wasu lokuta, yana kin tafiya. A cewar Cibiyar
Nazarin Ilimin Yara na Amirka (AAP), rikidewan idanu abu ne da ke iya faruwa da
idanun jarirai tun daga haihuwa har izuwa kimanin watanni 4. Dalilin haka
shi ne, idanuwan jarirai ba sa iya mai da hankali sosai a watannin farko na
rayuwa, wanda hakan ke sa idanuwansu zagayawa ba tare da wani kamewa ba,
wanda a wasu lokuta kan kai ga rikidewa ko fita waje ko ciki. Duk da
haka, idan hakan ya ci gaba bayan watanni 4, ya kamata ku tuntubi likitan
jaririnku.
A
cewar Cibiyar Kiwon Lafiya ta ƙasa, kusan kashi 4% na yara suna da idanu ɗaya
ko duka biyun da ba daidai ba watto ya rikide.
Abin takaici shine, strabismus baya tafiya da kansa. Hakanan yana iya
haifar da asarar gani na dindindin idan ba a kula da shi ba. Strabismus
kuma na iya haifar da bibiyu ga yara. Hakanan yana iya rinjayar gani,
tare da ikon gani a cikin girma uku ko tare da asarar zurfin fahimta
(stereopsis). Iyaye ko jagora na iya gano wannan cuta a cikin 'ya'yansu
waɗanda har yanzu ba sa iya yin magana game da matsalolin gani ba, ta hanyar
lura da yadda suke matse idonsu. Yaran da ke fama da strabismus kuma suna
iya juya ko karkatar da kawunansu don ganin abubuwa da kyau.
Idan ba a
kula da strabismus ba, kwakwalwa za ta yi watsi da hoton da ido mai rauni ya
samar, wanda zai haifar da amblyopia, ko "lazy eye." Amblyopia hasara
ce ta dindindin da ba za a iya gyara ta da ruwan tabarau ko tabarau ba.
Amma idan an gano strabismus da wuri, ana iya magance shi ta hanyoyin nan:
1. Rufe idanu
Rufe idon
da ke da raunin zai ƙarfafa jijiyoyin idon na tsawon lokaci, tabbatar da cewa
babu wani kaifin Gani da ya ɓace da kuma maido da daidaituwar ido.
Ya danganta da tsananin matsalar, yara za su sa facin watto Rufe idon na tsawon
sa'o'i 2-3 a kowace rana a cikin sa'o'in da idon su biyu na shekaru da
yawa. Ana iya Rufe idon na tsawon sa'o'i shida a kowace rana a wasu
yanayi.
2. Diga atropine.
Aikin
atropine kamar Aikin Rufe idon ne.
3. Gilashin
A
wasu yanayi, sanya tabarau na iya taimakawa wajen daidaita idanuwa, tabbatar da
cewa an samu alaƙa tsakanin kwakwalwa da idanu yadda ya kamata.
4. Hanyoyin tiyata.
Wannan hanya ita ce abu na ƙarshe da za a yi amfani da shi idan tabarau, digon magani, da Rufe idon sun kasa daidaita idanu.
Idan
kun ga wasu canje-canjen a idanu (ko rashin lafiya) a yaranku, kada ku
jinkirta zuwa asibiti.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment