Hutu lokaci ne na haɗin kai na musamman ga yawancin iyalai, alaƙa da
abubuwan tunawa da aka kafa yayin irin wannan yawon iyali . Yara kuma suna
koyan abubuwa da yawa daga ziyartar sabbin wurare da kuma hulɗa da mutane daga
wurare daban-daban.
Ga kaɗan daga cikin mafi kyawun wurare a Najeriya don ɗaukar iyali:
1. Obudu
Mountain Resort
Idan Kun kasance masu yawon bude ido ne masu neman kasada da
kwanciyar hankali, Obudu Mountain Resort na ku ne. An san shi a matsayin
mafi kyawu a Afirka kuma ɗaya daga cikin mafi kyawun wuri a Najeriya, wurin
shakatawan yana cikin tsaunukan da zurfin dazuzzukan na jihar Cross
River. Zaku ji daddin motocin kebul, hanyoyin tafiya na canopy da ƙari
tare da dangin ku.
2. Yankari
Game Reserve
Wuri ɗaya mai kyau a Najeriya don ɗaukar dangi shine Yankari Game
Reserve. Wurin da ke cikin Jihar Bauchi, yana da maɓuɓɓulan ruwan dumi na
yanayi da dama, da giwaye da zakuna a Nijeriya. Don nutsewa a cikin
maɓuɓɓulan ruwa masu ɗumi, kallon namun Daji, yawon bude idon dangin ku
zai zama abin tunawa.
3. Ikogosi
warm springs
Jerin kyawawan wurare a Najeriya ba zai cika ba, ba tare da Ikogosi Warm
Springs ba, daya daga cikin manyan wuraren shakatawa na Najeriya. Wajibi
ne a fuskanci abin al'ajabi na yanayi na haduwar maɓuɓɓulan ruwa guda biyu
yayin da suke kiyaye yanayinsu. Wannan wajan na bukatan ku saka takalman
tafiyan ku, kuma ku shirya kyamararku don ganin Abubuwan ban mamaki.
4. Idanre
Hill
Dutsen Idanre yana cikin wani tsohon birni da aka kafa akan wani tudu a
cikin garin Idanre Akure, jihar Ondo. Ku tabbatar cewa kun ɗauki matakai
682 da yake ɗauka don zuwa saman tudu domin ganin cikin kyakkyawan
yanayin birnin tare da dangin ku.
5. Olumo Rock
Dutsen Olumo wani katon dutse ne na dutsen granite. Dutsen
wani abin tunawa ne na tarihi wanda ya zama matsuguni ga mazauna wurin a
lokacin yaki. Idan yaran ba su iya haura zuwa saman dutse ba, akwai
na'urorin hawan don su iya kallon wannan kyakkyawan wurin a Najeriya.
6.
Erin-Ijesha Waterfalls
Erin-Ijesha Waterfalls tarin tudu guda bakwai ne da ke zubo da ruwa kan
wani dutse, wanda ya haifar da ruwa mai ban sha'awa kashi bakwai.
Kowane bangare yana samar da matakai bakwai daban-daban tare da kowane matakin
yana kayyatarwa. Da wannan aka ce, ruwan Erin-Ijesha tabbas wuri ne mai
kyau a Najeriya don fitar da iyali na kwana ɗaya daga cikin birni.
7. Zuma Rock
Zuma Rock wani katafaren tsauni ne a kusa da Babban birnin tarayya
Abuja. Wani lokaci ana kiranta da "Ƙofar Abuja daga Suleja",
Zuma rock wani katafaren yanki ne na halitta wanda ke yammacin Abuja babban
birnin Najeriya. Ku tabbatar kun tafi tare da ƙwararren ɗan tuƙi yayin
ziyartar wannan kyakkyawan wuri a Najeriya.
8. Lekki
Conservation Center
Idan dangi ku sun kasance masu son dabba, Cibiyar Lekki
conservation center ita ce mafi kyawun wurin da za ku ziyarta. Yin
tafiyan ƙasa mafi tsayin titin a Afirka, ku sami damar kallon tsuntsaye, birai,
da wasu nau'ikan dabobi a cikin wajan.
9. Mpape
Crushed Rock
Mpape Crushed rock dutse ne wanda aka yi watsi da shi a cikin
Abuja. Wannan kyakkyawan wuri a Najeriya, don yin picnic tare da
iyali, daukar hoto, ko tafiya mai daɗi. Shirya kwando, saka wasu takalmi
masu daɗi sawa, kuma ku nufi wannan wajan mai cike da al'ajabi da ban mamaki.
10. Awhum
Waterfalls
Ruwan Awhum yana samuwa ne daga wani katon dutsen da ruwa ke
gudana a saman sa, ya kuma kafa rafi. Mafi kyawun lokacin ziyarta shine
lokacin damina don haka ku tabbata kun shirya tufafi masu daɗi da takalmi kuma
ku kasance cikin shiri don zaku ɗan jike yayin da kuke yawan bude ido a wannan
kyakkyawan wuri a Najeriya
Daga: Firdausi Musa
Dantsoho
No comments:
Post a Comment