Hadaddiyar hanyar hada salak in Najeriya na gargajiya salad mai daddi. Salak na da launi mai kyau, yana cike da abubuwan gina jiki, yana da kosarwa sosai kuma yana da daɗi . ana iya cin salak ta hanya daban daban ana iya cinsa a matsayin appetizer, ko azaman babban abinci mai daɗin gaske kuma yana da sauƙin hadawa. A zahiri salak abinci ne da ke tafiya a kowani lokaci.
Kuyi la'akari da cewa kayan lambun ba dole ba ne
su kasance masu ganye don cancantar kasancewa
cikin salak.
Wannan Salak mai dadi ya kunshi kayan lambu danye da dafaffe, taliya, Kwai da
sauransu. Tare da duk waɗannan sinadaran, tabbas wannan Salak akansa abinci ne mai daɗi amma kuma ana
iya haɗa shi da shinkafar Jollof, Fried rice, Soyayyen kaza da sauransu.
Abubuwan mafi
muhimmanci da ake amfani da
su wajan hada salak sune Letus da Kabeji amma suna kewaye da Tumatir,
taliya, Kwai, Cucumber, Wake da masaran gwangwani. Duk waɗannan sinadarai suna
sa wannan salak in ya zama ya kayatu don nishadantar da jama'a kuma kamar tare
da yawancin salads, yana da sauƙi. Misali, ana iya amfani da dankalin turawa a
madadin taliya.
Abubuwan bukata wajan
hada salak
* Karas 2
*Kofuna 2 na yankakken letas
*Kofuna 2 na yankakken Kabeji
*Tumatir biyu mai kwari
*Kofi 1 na taliya ko dafaffen dankali
* Dafaffen Kwai Manyan
2
*Cucumber Matsakaicin Girman
guda 1
*Waken Gwangwani
*Masarar gwangwani
*Babbar
cokali 8
na Heinz Salad
Cream
Yadda
ake hadda salak
1.
Ki shirya kayan lambun ki duka sai ki wanke su sosai cikin Ruwa mai
gudana.
2.
A dafa kwai a kuma tafasa Taliya da gishiri kadan har sai ya dahu.
3.
Sai ki yanka kabejinki da latas, ki yanka tumatur din ki
yanka kananan, kina iya gursa
karas dinki ko ki yanka su
kananan ki kuma yanka Cucumber inki shima.
4.
Sai ki zuba komai a cikin kwano mai tsafta banda kwai da Cream sai ki rufe shi da roba ko murfi mai matsewa sai a saka a
cikin firiji na akalla awa 1.
5.
Bayan awa daya sai a cire shi daga Firji lokacin da aka
shirye yin
amfani dashi,
sai a chakuda su tare a sa ƙwai
da aka
dafa akan salak in. Sa a
hada tare da cream in salak na Heinz .
6.
A ci lafiya.
By:Firdausi
Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment