Ya zama ruwan dare a cikin al'ummar nahiyar Afirka iyaye kan yi wa
'ya'yansu bulala don sun yi fitsarin kwance wanda abu ne da ya zama ruwan dare
a yawancin yara yayin da suke girma. Wani lokaci, waɗannan dabi'ar
na tafiya da zarar yaro ya girma.
Amma rikice-rikice da yawancin yara ke yi a wannan lokacin na
rayuwarsu yana da yawa kuma mafi yawan lokuta suna fushi sosai. Amma ba
kyau iyaye su mayar da shi al'adar yin wa 'ya'yansu Duka a duk lokacin da suka
yi fitsarin kwance.
Akwai wasu hanyoyin da zaku iya bi a matsayin ku na iyayen don
taimaka wa yaranku shawo kan wannan matakin ba tare da dukansu ba.
1. Canja lokutan shan Abubuwan shan su
Ku sanya fifikon yaranku su sha isasshen ruwa da rana. In zai yiwu
a sanya ruwa a cikin goran ruwan yaranku lokacin da za su je makaranta,
wannan shine don taimaka musu shan isasshen ruwa da rana da rage shan ruwa da
yamma.
Wannan yana taimakawa wajen hana yaranku yin fitsarin kwance
saboda za su sami ƙarancin ruwa a jikinsu a cikin dare.
2. Sanya wa yaranku lokutan shiga bandaki
Hakan zai taimaka wa yaranku su koyi al'adar yin fitsari a cikin
awanni biyu zuwa uku kafin barci. Idan za ta yiwu, za ku iya tashe su da
dare kuma ku taimaka musu su je banɗaki.
3. Ku Kasance mafi ƙarfafawa kuma mai yiwuwa a gare su
Idan yaron ku ya fara samun ci gaba kamar daina yin fitsarin
kwance na mako guda ko fiye, sai ka mayar dashi al'ada a ko da yaushe taya su
murna, wannan yana ba yara damar samun nasara kuma yana sa su zama masu himma.
4. Ku guji barin yaran ku suna yawan jin kishiruwa
Kada ku sanya yaranku su ji kishiruwa ko da na sa'o'in, domin kuwa
hakan yana iya sa su shan ruwa da yawa da daddare wanda zai iya sasu
fitsari lokacin da suke barci.
5. Kar da ku hukunta Yaron ku don Yayyi fitsarin kwance
Duk yadda abin zai kasance da takaici a farkon lokacin da kuka
fara wannan matakin, kada ku yi amfani da hukunci saboda yawancin lokuta ba ya
aiki.
By Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment