zamani ya canza da za a ba da budurwa aure ba tare da
la'akari da ko saurayin ya dace da ita ta kowace hanya ba. Iyalan
budurwar sun fi damuwa da cewa ta kai mizilin yin aure. A wannan halin da
ake ciki, tana iya yin sa'a ko rashin sa'an mijin aure. A sakamakon haka, za ta
dage da nuna farin ciki koda tana shan wahala.
Amma, kamar yadda yake
a yanzu, abubuwa suna canzawa cikin sauri. Kuma abubuwa ba daya suke ba kamar
yadda suke a da. A sakamakon haka, zaku iya ganin budurwa wacce ta kai yin aure
tana ɗaukar lokacinta don gujewa yin zaɓin da bai dace ba na abokin zama a
kwanakin nan.
A sakamakon haka, a
matsayin ki na mace, ga abubuwa guda hudu da dole ne namiji ya kasance
dasu kafin ki yarda ki aure shi;
1. Ka tabbatar yana
sonki da gaske:Mutumin da yake ƙaunar ki da gaske zai yi tunani sau biyu kafin
ya cutar da ke ko ma ya yaudare ki. Zai fifita ki domin ya damu da ke da kuma
alakar da ke tsakanin ku. Lokacin da kika auri mutumin da ba ya son ki, ba zai
yi jinkirin bibiyan yan mata tare da yaudarar ki da kusan kowace mace
kyakkyawa da ta zo masa ba. Kafin ya cutar da ke kuma ya tozarta ki ga wahalar
da tsananin damuwa, ba zai yi nazari ba. Amma idan yana ƙaunar ki da
gaske, za ki zama abu mai ƙima a gareshi wanda ba zai so yayyi asara ba.
2. Dole ne ya kasance
mai tunani da nazari yadda ya kamata: Kamar yadda ake cewa, ba a ayyana balaga
ta mutum da shekarunsa. A sakamakon haka, kawai saboda mutum ya bayyana yana da
shekaru 30 ko 40 baya nuni da cewa ya balaga kuma yana iya magance ƙalubalen
rayuwa. A sakamakon haka, a matsayina ki na budurwa, dole ne ki kasance mai
lura da alamun cewa yana da nasari, tunani, kafin ki yarda ki aure shi.
Idan akasin haka ne, laifin ki ne.
3. Dole ne ya kasance
yana da hanyar samun kudin shiga na halal: Lokaci ya wuce da ake tilasta
wa budurwa shan wahala tare da mutumin da take so ta aura. A wannan
zamani, dole ne ku tabbatar da cewa yana da ikon kula da ku da yaran ku. ku
tabbatar cewa zaku iya kula da kan ku ko yana kusa ko baya kusa.
4. Dole ne ya zama
mutum wadda zai fahimce ki:Fahimtan juna yana da muhimmanci tsakanin masoya. Za
a yi ta fuskantan matsaloli a kai a kai idan babu fahimta. A sakamakon haka, dole
ne ki tabbatar cewa ya fahimce ki kamar yadda kika fahimce shi ta fuskokin
abubuwan da yake so da abin da ba ya so. Lokacin da kuka fahimci juna da abokin
tarayya za ku iya magance matsaloli yayin da suka taso maku.
By: Firdausi Musa
Dantsoho
No comments:
Post a Comment