Menene shayarwa?
Shayar da nono lokacin
da ake ciyar da jariri madaran nono, kai tsaye daga nono. Ana kuma
kiranta raino. yanke shawarar shayar da nono lamari ne na mutum. Haka zalika
yana iya jawo ra'ayoyi daga abokai da dangi. Yawancin kwararrun
likitocin, ciki har da Cibiyar Nazarin Ilimin Yara na Amurka (AAP) da Kwalejin
Kwararrun Likitoci da Likitocin mata, suna ba da shawarar sosai ga shayar da
zallan Ruwan nono na musamman, babu madaran gwangwani, 'ya'yan itace, ko
ruwa na tsawon watanni 6. Ko Bayan fara basu wasu abinci, sun ba da
shawarar ci gaba da shayar da nono a gabaki daya farkon shekaran jariri.
Sau nawa ya kamata ku shayar da
jariri nono ya danganta da ko jaririn ya fi son cin abinci kadan, ko akai akai
ko yana daukan lokaci mai tsawo wajan cin abinci. Hakan zai canza yayin da
jaririn ku ke girma. Jarirai galibi suna son cin abinci kowane sa'o'i
2-3. Idan suka kai watanni 2, suna cin abinci kowane sa'o'i 3-4 ,
kuma idan suka kai watanni shida, yawancin jarirai suna ci abinci a kowane
sa'o'i 4-5. Ke da jaririn ki na musamman ne, kuma shawarar Shayar da nono
ya rage gare ki.
Alamomin
da ke nuna Jaririnki Yana jin Yunwa
Daya daga cikin hanyoyin da za ku fi
sanin cewa Jaririnku suna jin yunwa shine kuka. Sauran alamun da ke nuni da
cewa jaririn ku na bukatar abinci sun haɗa da:
*Lasar leɓunansu ko fitar da harshe
*Motsa bakin su, ko kan su don neman
nono.
*Saka hannun su cikin bakin su.
*Bude bakinsu
*Tsotsar duk abun da yazo kusa da
bakin su abubuwa.
Amfanin shayar da zallan Nono Ga
Jariri
Madarar nono na samar da abinci mai
kyau ga jarirai. Yana da kusan cikakkiyar hadin bitamin, furotin, kitse dama
duk abin da jaririnku ke buƙata ya girma. Kuma duk an bayar da shi a cikin
tsari mafi sauƙin narkewa fiye da tsarin madaran gwangwani.
Madarar nono tana
ɗauke da sinadirai wanda ke taimaka wa jaririn yaƙi da ƙwayoyin cuta na
bacteriya. Shayar da nono yana rage haɗarin kamuwa da ciwon asma ko rashin
lafiyan. Haka kuma, shayar da zallan nono na musamman ga jariri na tsawon
watanni 6 na farko, ba tare da wani tsari ba, yana kawo kawar da matalar ciwon
kunne, cututtukan numfashi, da kuma zawo. Yana kuma rage tafiye
-tafiyen zuwa asibiti ganin likita.
An danganta shayar da nono da
kara ƙimar ƙwaƙwalwa mafi girma a cikin ƙuruciya a lokacin karatun. Haka
zalika, kusancin jiki, fata-da fata, da kallon cikin kwayan ido duk suna
taimaka wa jaririn ku kara kusanci da ku, kuma ku sami kwanciyar hankali.
Jarirai da ake shayarwa sun fi samun nauyin da ya dace yayin da suke girma
maimakon zama yara masu kiba. AAP ta ce shayarwa kuma tana taka rawa wajen
rigakafin SIDS (cutar mutuwar jarirai kwatsam). An bayyana cewa yana rage
haɗarin kamuwa da ciwon sukari, tsananin kiba, da wasu cututtukan daji, amma
ana buƙatar ƙarin bincike akan haka.
Amfanin
shayar da zallan Ruwan Nono Ga Uwa.
Shayar da jariri Nono yana ƙona ƙarin adadin
kitse, don haka zai iya taimaka muku rage kiba da kukayi lokacin da kuke da
ciki da sauri. Yana fitar da sinadarin oxytocin, wanda ke taimakawa mahaifa ta
koma yanayin girmanta na da kafin daukar ciki kuma tana iya rage zubar jinin
mahaifa bayan haihuwa. Shayar da nono kuma yana rage haɗarin kamuwa da cutar
sankarar mama dana mahaifa. Yana iya rage haɗarin ku na kamuwa da osteoporosis.
By:Firdausi Musa Dantsoho