Friday 29 October 2021

Lemun tsamiya

Shin kuna bukatan lemu wanda keda dan karan dadi mai kuma dan zaki zaki da tsami tsami mai dadin sha? Lemun tsamiya lemu ne daya banbanta da sauran lemo a dandano, gashi da dadin sha tare kuma da wanke ciki batare daya cutar da mutum ba. Ana samun tsamiya sosai anan arewacin Nigeria, yan arewa sunfi amfani dashi.

Yadda ake hada lemun tsamiya.

Da farko dai za mu samu tsamiyan mu mai kyau ,sai mu bare tsamiyan, sai mu dora tukuna a cikin tukunya

A saka tsamiyan a cikin tukunyan ruwan, sai a tafasa har na minti goma.

Sai a barshi cikin tukunyar har yayi sanyi

In har an tabbata cewar yayi sanyi, sai a zuba shi cikin blender a markada shi sama sama, ana yi ana zuba ruwa daidai yadda ake so.

 

Bayan wannan, sai a dauko mataci a tace ruwan da tsakin tsamiyan, za a iya matsa lemon a ciki in har ana bukata

Daganan za a iya saka sugar ko zuma in ana bukata, sai a saka a fridge domin yayi sanyi.

Za a iya shan lemun tsamiya da kowane irin abinci,ko ma haka kawai don shakatawa.

Daga Maryam Idris.

 

No comments:

Post a Comment