Tsohuwar Jarumar masana’antarshirya fina-finan
hausa ta kannywood, Mansura Isa ta yi ƙorafin tare da nuna rashin jin dadin ta
bayan da shugaba Buhari ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga mawaki
Abdulganiyyu da aka fi sani da Sound Sultan ta hannun Femi Adesina.
Tsohuwar jaruman ta bayyana hakam a shafin nata na
Instagram inda ta wallafa rubutu kamar haka; Baba Buhari, tin da a ke mana
Mutuwa a Kannywood ba ku taɓa mana jaje ba, ko gaisuwa na rashi ba. Amma duk
sanda yan Kudu wani abu ya samesu ku ne na farkon jaje.
In baku jawo naku a jiki ba, wa za ku ja jiki ? Masu girma Dr Zainab Shinkafi da Mamanmu Aisha Buhari ne kadai su ke bamu goyon baya kuma muna yaba musu.
Amma za mu ji dadi in ka nuna mana ƙauna muma Baba Buhari.”
Mansura ta cigaba da cewa; Mu ne ku fa, duk Alheri da muka samu AREWA muke kawowa domin a amfana. Dan Allah a duba wannan Abu Baba.
Daga ƙarshe dai Mansurar ta ce ta karkata akalar sakon zuwa Bashir Ahmad, daya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Buhari a fannin yada labarai.
“Bashir Ahmad, kai ne ya kamata ka yi wannan, domin shima Adesina yana gyara nasu mutanen. Kuma ina da yakini cewa kasan irin gwagwarmaya da muke wa gwamnatin nan, duk da zagin mu da a ke yi a kanku. Dan haka muna jiran sakon ta’aziyyarmu ga wadanda muka rasa musamman ta mamanmu Haj Zainab Booth.
Marubuciya: Firdausi Musa Dantsoho
No comments:
Post a Comment